Siffofin Yadda Ake Gane 'Yan Luwadi Da Illolinsu Cikin Al'umma - Android Pols

Siffofin Yadda Ake Gane 'Yan Luwadi Da Illolinsu Cikin Al'umma - Android Pols
Siffofin Yadda Ake Gane 'Yan Luwadi Da Illolinsu Cikin Al'umma


Siffofin Yan Luwadi Da Rayuwarsu Cikin Al'umma, Dan Haka Mu Kula Da 'Ya'yanmu Da kannanmu 


Ba tare da bata lokaci ba kowa dai ya san ma'anar Luwadi wanda girman laifinsa a musulunci shine kisa, kisan ma na wulaknaci. Don haka kai tsaye zan tafi zuwa ga zayyano muku siffofin 'yan Luwadi, yadda za'a ganesu a cikin al'umma da kuma bayani akan rayuwar 'yan Luwadi cikin sirri. 

1- Siffa na farko da za'a fara gane ɗan Luwadi shine ɗan daudu, idan sun rika a harkan luwaɗi sai su fara yin shiga irin na mata, da magana irin na mata, da duk wata mu'amala irin na mata. Duk ɗan daudu ana zuwa masa ta dubura.

Luwadi kashi biyu ne: akwai nau'in Luwadi da ana yin amfani da wasu mayukan shafawa a goga a tsakanin cinyoyin namiji a na yin lalata dashi ba tare da an je ta dubura ba, wasu basa yarda ayi ta dubura saboda suna tsoron kada a zuba musu cuta, shiyasa ko da an kamasu, idan anje gwaji likita zai ga ba'a batawa ɗan luwadin dubura ba, amma dai ana Luwadi dashi ta tsakanin cinyoyinsa, sai kuma wanda ake zuwa ta dubura.

2- Idan baka taba haduwa da dan luwadi ba, sai kuka fara haduwa a karon farko, ka lura da idonshi yana zuwa gabanka (saitin al'aura) zai fara kallo kafin ma kuyi musabaha, domin su 'yan Luwadi a rayuwarsu basa sa gajeran wandon ciki, kamar boxer haka, ta nan ma suna saurin gane junansu idan haduwa bata taba hadasu ba, idan kun gaisa hannu da hannu da ɗan luwadi zai matse maka hannu da karfin tsiya, sannan ya kura maka ido, wannan wata hanyace da 'yan Luwadi suke gane junansu da wuri.

3- Suna da wata siffa na kyautatawa wanda suke so suyi Luwadi da shi, shiyasa ko da an kama ɗan Luwadi zaku ga mutane suna jin nauyin a masa rashin mutunci a unguwa saboda yadda suke kyautatawa yara, sannan matsananciyar shakuwa, kullun suna tare. Magidanci idan kaga kullun yaronka matashi yana tare da abokansa, idan dare yayi su yi wanka su fita to akwai wani abu. 

Suna da zumunci a tsakaninsu kamar zumunci irin na kurame da bebaye, iyaye sai ku sa ido, sai su samu yaro karami suna kyautata masa, to ko da sunja yaro cikin daki sun fara tabashi, idan yaron yaki yarda ya fita ba zai tona musu asiri ba, saboda yana tunanin wannan kyautatawar da suka mishi a baya, basa shigar da bukatarsu har sai sun tabbata ya gama sakin jiki da su, kuma idan ankai wannan matakin ba dole yaro ya tsallake tarkon su ba

4- Harkan bikin ranar haihuwa (birthday), jama'a kuji tsoron wannan harka ta birthday da ake yi yanzu, yaro matashi ɗan shekara 20 bai da sana'ar komai amma zai je ya kama hayar babban gurin taro ko shakatawa ya shirya gagarumin biki saboda ranar haihuwarsa, to yawanci irin wannan yara manyan attajirai abokan harkansu na luwadi ke daukar nauyinsu, kuma anan zasu je su ga sabbin yara matasa, a fara shigar dasu harkan luwadi, haka yake a tsakanin 'yan mata da abokansu na Madigo game da batun shirya birthday.

5- Sirri: Akwai kungiyoyin 'yan Luwadi a unguwanni, makarantu, kasuwanni, guraren sana'o'in matasa da sauransu, suna da kungiya, to amma suna da siffa na tsananin rikon sirri sosai, a cikin kungiyar har mukamai suna da shi, idan an ga matasa masu matsakaicin shekaru suna yawan zama a majalisa daya, kuma suna son junansa, idan wani yazo gurin suna canza hira, akwai bukatar saka ido a kansu don sanin hakikanin mu'amalarsu.

6- 'Yan Luwadi suna da wata siffa na yin soyayya tsakanin na miji da na miji, har siyayyar kayayyaki suna yiwa juna, kamar dai yadda akeyi a tsakanin mace da na mijin da suke yin soyayya da zata kai su ga yin aure. Kuma har alkawari ake tsakanin 'yan Luwadin da suke yin soyayya, cewa ba zai kula kowa ba, amma zai dauke masa dukkan nauyi da bukatu kamar miji da mata, banbancin kawai shi ba zai tare a gida ba.

7- Daga cikin siffofin 'yan Luwadi da zaku gane suna kiran taro amma cikin wata irin siga da idan ba kai memba bane a cikin kungiyar ba zaka gane ba, yau zan fasa muku sirrin, duk inda kukaji 'yan daudu sun kira taron "ajo" to auren wani zasu je su daura, taro ne na 'yan luwadi

8- Yana daga cikin siffofin 'yan Luwadi kin yin aure tsakanin mace da na miji, saboda bincike ya nuna mana duk azzakarin da ya saba da shiga dubura maimakon farji, to azzakarin na gogewa, ta yanda daga baya ko da ya shiga farjin mace ba zai taba jin dadin jima'i ba sai dai ta dubura, shiyasa duk wani 'dan luwadi bai son a masa maganar aure ma, kuma za'a ga yana da halin yin auren, da kuma lafiya amma yaki aure.

9- Duk 'dan Luwadi da ake zuwa masa ta dubura kuma yayi nisa a harkan, to zaka ga baya iya zama akan kujera kamar yadda mutanen da ba'a luwadi da su ke yi, shi ɗan luwadi idan yazo zai zauna kan kujera sai ya karkace, saboda yana tsoron kar wani ruwa ya zubo masa ta dubura, haka ɗan luwadi baya iya tsayuwa a tsaye ya bude kafafunsa, saboda an fafuke masa dubura yana tsoron fitar ruwa, shiyasa baka rasa rikakkun 'yan luwadi da auduga ko kayan tare jinin al'ada irin na iyaye mata, saboda shima yana toshe duburarsa daga fitar ruwa mai wari wanda kudaje na iya binsa a cikin jama'a

10- Idan an zubawa na mijin da ake luwadi dashi maniyyi a dubura, maniyyin baya bin jikinsa ya wuce, saboda Allah (T) bai halacci jikin ɗa namiji don a zuba masa maniyyi ba, (ba kamar mace bane da zai wuce mahaifa da sauran jikinta har ma ya kara mata lafiya) don haka maniyyin taruwa yake a duburan ɗan Luwadi, a hankali sai ya rube, ya haifar da wasu tsutsotsi, wadannan tsutsotsin abincin su shine maniyyi, idan ba'a zuba musu sun sha ba, sai su fara cizon duburar ɗan luwadi, ba zai taba samun lafiya da kwanciyar hankali ba sai yaje anyi Luwadi da shi, wannan siffar su ce.

11- Siffofinsu a dandalin Facebook: yanzu facebook jama'a ya zama kamar don 'yan Luwadi akayi, duk wani ɗan Luwadi yana yin facebook da WhatsApp, kuma sun san yadda suke haɗuwa, suna da wani yare da sukeyi a wannan dandali na facebook, suna kiran sunan Luwadi da kalmar "harka", azzakarin 'da na miji suna kiransa da "lemo", dubura suna kiransa da "birni" wato idan zasu tambayeka shine zasu fada maka haka, cewa; kai birni ne? wato ana zuwa maka ta dubura?, wanda ya rika a harkan kungiyar Luwadi har ya zama jagora suna kiransa da suna "mai garwa". 

Idan kai luwadin da ake zuwa wa ta cinya ne, kamar yadda nayi bayani a farko, suna kiransa da "kauye" wato zasu tambayeka kai birni ne ko kauye? ma'ana ana zuwa maka ta dubura ne ko ta cinyoyi? Idan sun ma wannan tambayar ta Facebook suka ga baka gane ba to sai su kyale ka, saboda sun san baka san harkan ba, wato kai ba ɗan Luwadi bane. Wannan babban alamace da zaku gane 'yan Luwadi a wannan dandali na facebook. 

Jama'a Watannin baya na taba tarwatsa taron gamayyar 'yan Luwadi da Madigo na Facebook a wannan dandali, shine sai sukayi taron dangi don su bani tsoro sannan su lalata min Facebook account, amma dai Allah bai basu nasara ba har yau 

Mu hadu a rubutu kashi na biyu, idan ta kama zan fitar muku da wasu abubuwa da hotuna na bincike don ku fahimci irin mutanen da muke tsananin kiyayya, gaba da adawa dasu kamar yadda 'yan ta'adda basa so

Sakon dake kan wannan hoto nassin Qur'ani ne, inda Allah Madaukakin Sarki yake cewa; "Ku ji tsoron ranar da zamu taso ku zuwa gaban Allah, domin a bawa kowace rai sakamakon abinda ta aikata ba tare da an zalunceta ba".

Allah Ka shiryar da 'yan Luwadi da Madigo, wadanda ba zasu shiryu ba Allah Kai kasan abinda Ya dace dasu, Ka tsare al'ummar musulmi daga sharrin


Daga Engr Danladi Safiyanu Hayin Banki Kaduna

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

11 Comments

  1. 𝘞𝘢𝘯𝘯𝘢𝘯 𝘮𝘢𝘨𝘢𝘯𝘢𝘳 𝘨𝘢𝘴𝘬𝘪𝘺𝘢 𝘯𝘦 𝘸𝘢𝘭𝘭𝘢𝘩𝘪

    ReplyDelete
  2. ALLAH karabamu da mummunar qaddara, masuyi kuma ALLAH ya shiryesu.

    ReplyDelete
  3. YA Ubangiji Ka Kin'tsama'na Shiriya Acikin Zuciyar' mu , Kuma Ka Kare'mu Daga SHARRIN Kan'mu da Kan'mu da Zuciyar' muu Amin ya rabbil'Alamin

    ReplyDelete
  4. Allah yashiryemu ya shiryamana yara Amman gaskiya kaima Dan luwadinne Dan inbacikinsu kakeba ya za ai kasan haka

    ReplyDelete
  5. Ai inkaji yandaudu sunacewa wanan shudane to suna nufin baida Ido inkaji ance baka da Ido to baka harka inkaji ance wannan yanada Ido to Yana harka kuma sun tsani kacemusu Yan daudu sedai kace Meka insukaji kace Meka to kanada Ido har asiri sunawa Wanda sukeso kamar yanda budurwa kewa saurayi inkaji since shagwa to saurayinsu kenan sunacewa harka shiyasa basa kyamar harkar dazasu dinga kiranta luwadi sesun tsani harkar duwanda kaga Yana haba haba dakai kana zargin Dan luwadince fara gogamar magana kana nunamasa mene ribar Dan luwadi kaikam baabin dazesa kayi luwadi nama Imani da Allah sekaga yayi sanyi dakai ka gwada a fcbk sunaduba friend din junan su koda bakayi insukaga yawan friend din dake tsakaninku to zasu biyoka hanyoyin nada yawa sedai Allah tsaremu

    ReplyDelete
  6. To ubangijin Allah yashiga tsakaninmu dasu

    ReplyDelete
  7. Allah ya mana tsari da wannan qazantar.

    ReplyDelete
  8. Me Wannan rubutu yana bukatar kara yin nazari da bincike sosai game da kwayar halittar dan adam meke kawo wasu sıffofin mata ga namiji haka meke kawo siffofin maza ga ya mace rashin adalci ne idan kace duk dan daudu yana luwadi Sabida asalin daudun Menene shi?
    Neman suna ne kawai kakeso Shiyasa ka fito ta Wannan tsigar maganar shakuwa sakanin jinsi kuwa Wannan sabo ne shike kawo hakan domin Akwai shakuwa na yanuwanta zuwa abota wanda kuma babu sabawa Allah a cikinsa face zumunci shi me ilimi baya yanke hukunci kai saye face Sai yayi bincike me zurfi ya samu hujja akan abinda zai fadi. Amma Kai daga farkon fari saika rusa bayanın naka domin kayi jamau akan yan daudu a karshe dai abinda zance shine mu Taru mu godewa Allah dayasa zunubi baa zubutashi a fuska da wallahi dayawan jamaar arewa musulmi sun dena fita domin kuwa Wannan harkar ta zama gıdan kowa harda gidanku ma don haka addua shine mafita masuyi Allah ya shirya wanda basayi Allah ya tsare amen

    ReplyDelete
Previous Post Next Post