Yadda Za Ki Iya Bambance Discharge Da Gano Abin Da Ya Kawoshi - Android Pols

Fati Washa: Yadda Za Ki Iya Bambance Discharge Da Gano Abin Da Ya Kawoshi - Android Pols
Yadda Za Ki Iya Bambance Discharge Da Gano Abin Da Ya Kawoshi 


Hanyoyin Yadda mata za su iya  Bambance Discharge Da Gano Abin Da Ya Kawoshi 


Kamar yadda na fada a baya fara gano abin da yakawo infection shine babban abin da likita ya kamata ya fara sani kafin Dora mutum akan magani 


1. TRICHOMONAS, (bacteria ce) ita kuma discharge din da yake jawowa shine yana kore ko yellow ne haka sannan yana nuna symptoms dinsa ne haka kamar karnin Kifi kuma ga kaikayin tsiya.

2.CANDIDIASIS (Yeast infection).shi kuma discharge dinsa fari ne mai kauri, mai kamar farin madara, yawanci yafi faruwa ne kafin mace taga period dinta. Sannan yana da alamomi kamar su kaikayi da jin zafi zafi ta ciki da ta waje. 

3.BACTERIAL VAGINOSIS :-shi ma infection ne da yake jawo discharge kamar toka toka (grey white) sannan yana sa warin gaba kamar karnin Kifi kifi haka. 

4.STIs (sexual transmitted infections) kamar su gonorrhea, chylamydia da sauransu. Duk suna jawowa mace taga farin ruwa a gabanta sannan yawanci su bama sa da wani specific symptoms da ake gane discharge dinsa sai dai idan aka je lab. Sannan discharge dinsu yana nan kamar diwa diwa haka.

Duk sanda kika ga farin ruwa yana fita daga gabanki fari ne milk ne mai kauri ne, Salala ne, mai yauki ne ko mai Santsi ne, muddin baya wari ko sa kaikayi ko jin zafin gaba yayin fitsari ko yayin saduwa da namiji Salin alin yake fitowa rabinsa, to Karki damu kanki babu matsala. 

Masha Allah insha Allah kamar yadda na fada dama zamuyi jawabi daidai gwargwado Akan lafiyar matanmu/kannenmu to alhamdulillah nasan ko yanzu an karu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post