Yawancin Mata Suna Son Auren Maza Da Suke Da Wadannan Halaye Guda 5


Idan ana maganar zabar abokin rayuwa, yawancin mata suna zaɓar wasu halaye na maza. Kafin amincewa da yin soyayya da namiji, mata suna duba wasu halaye da suka dace da tsarin su. Kuna iya mamakin dalilin da yasa macen da kuka dade kuna tare ta ki amincewa da batun auren ku.


Yana yiwuwa ba ku da duk halayen da zan lissafa a wannan rubutun. Kudi ba lallai ba ne ya zama abu mafi mahimmanci ba. Yawancin mata masu ɗabi'a da mutunci suna zaɓar abokan rayuwarsu bisa wasu dalilai fiye da kuɗi, koda kuwa kuɗi yana da mahimmanci a cikin zamantakewar rayuwa. 


Don haka ne na zaɓi na rubuta muku wannan halayen na wasu mazan da mata suka fi so da burin samu domin yin aure. 


1. Namiji Wanda zai iya kare su. 

Ko da sun yi kuskure, mata suna son namijin da zai tsaya musu a fili. Mata ba sa son su auri mutumin da zai rabu da su wanda ba zai iya Kare musu mutuncin su ba. 


Wasu mazan suna kasa kare abokan zamansu mata a bainar jama'a. Idan matarka ta yi kuskure, to ka tabbatar ka tsaya mata a gaban wasu kuma ka yi mata gargad'i mai tsauri da gyara a sirrance. 


2. Wanda zai iya yi musu nasiha

Yawancin mata suna son samarin da za su jagorance su kan hanya madaidaiciya kuma su yarda da duk wani shawarar da suka yanke a rayuwa. 


Budurwarku tana buƙatar ganin ku a matsayin misali a gare ta. Ba ka son matarka ta nemi shawara daga wasu mazan yayin da kake kusa da ita a matsayin mijin aure. 


3. Mai girmama su

Mata suna son namijin da zai girmama su da ganin kimar su, kamar yadda maza suke yi. Yawancin mata suna son su auri namiji mai daraja ra'ayinsu kuma yana da hankali a rayuwar yau da kullun. 


4. Mutum mai rikon amana

Ko da yake yana da sauƙi a faɗi, amincewa yana da wuyar samu ga wasu mutanen. Mata kuma, suna son abokin tarayya da za su dogara da su kuma su rike musu amana na tsawon rayuwarsu.


5. Mai taimako

Yawancin mata suna ɗaukar wannan a matsayin ɗaya daga cikin halaye masu mahimmanci a cikin rayuwar ma'aurata. Maza da yawa ba su da ilimin da ya dace don taimakawa abokan zamansu mata. Yawancin samari ba za su ƙyale matansu su yi abubuwan da suke da kyau da kuma so ba.


Wannan sune halaye biyar wanda yawancin mata suke son samun namiji dasu. Akwai matan da su ba kudi ne damuwar su ba, su kawai kulawa, kariya, taimako da kulawa suke bukata daga wajen namiji. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

  1. Masha Allah
    Allah yasa da mu da mata masu sanmu mu Kuma
    Allah ya hore mana abin kyautata musu ameen

    ReplyDelete
Previous Post Next Post