Rundunar tsaro a jihar Bauchi sun yi nasarar kame wata mata da ake zargin ta da shiga asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa inda ta sace wani jariri sabuwar haihuwa.
Matar mai suna Hauwa Ibrahim Khalid ta shiga asibitin ne a ranar Talatar da ta gabata inda ta shiga dakin da jaririn yake ta dauke shi ba tare da kowa yasani ba.
Jaridar Punch ta rawaito cewa ana zargin matar da yin amfani da kayan likitoci inda kai tsaye ta shiga asibitin har dakin da jariran suke ta dauke shi.
Wata majiya ta shaida wa Punch cewa matar ta saci jaririn ne a sakamakon gorin da iyayen mijinta suke yi mata na rashin samun haihuwa wanda hakan yasa ta yanke shawarar sato jariri ta kai shi garin su na Dull a cikin karamar hukumar Tafawa Balewa tana ikirarin danta ne.
Sai dai matar ta bayyana cewa tana cikin tashin hankali da damuwa na rashin samun haihuwa wanda hakan ya jefa ta yin wannan aika-aikar.
Wannan dai ba shine Karo na farko da ake samun mata suna zuwa asibiti suna sato jariri ba a dalilin rashin samun haihuwa. Ko a shekarar bara irin hakan ta faru a jihar Kano inda wata mata tare da taimakon mijinta suka je asibiti suka sace wani jariri sai dai daga bisani asirinsu ya tonu.