Saudiya ta haramta yin wasu abubuwa 8 a Makkah da Madina saboda Ramadan

Saudiya ta haramta yin wasu abubuwa 8 a Makkah da Madina saboda Ramadan
Saudi Arabia 


Saboda gabatowar watan Azumin Ramadan, Saudiya ta haramta yin wasu abubuwa 8


Kasar Saudi Arabiya ta haramta yin wasu abubuwa takwas saboda karatowar Azimin Ramadana.


 Abubuwan da aka haramta sun hadar da :-


1. kashe lasifika lokacin sallar a’sham.


2. An hana yada bidiyon sallar asham da ta tahajjudi a kafafen yada labarai a duk fadin duniya.


3. An Haramtawa masu yin i’itikafi a masallaci har sai an tantancesu.


4. Sanya dokar takaita sallar dare da ake yi lokacin azumi don kowa ya koma gida da wuri saboda a samu jam'in Asubah.


5. An hana neman taimako ko tallafi a harabar masallaci da wasu keyi don bada buda baki a cikin azimi.


6. An hana iyaye zuwa masallaci da yara, inda aka bukaci masu Yara su barsu a gida.


7. An dai na yin buda baki a farfajiyar masallacin Makka da Madina.


8. Bada umarnin kashe lasifika ko Kuma rage sautinta.


Shin yaya kuke kallon wadannan abubuwan da hukumomin kasar Saudiya suka haramta? 


By Mubarak Ubaye Kofar Wambai


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

  1. Da Bayahude ne Sarkin macca dole ya goyin baya Yahudawa
    Ya Allah na ganisa sa

    ReplyDelete
Previous Post Next Post