Gaskiyar Dalilin Da Yasa Aka Saki Murja Ibrahim Kunya Daga Gidan Yari

Gaskiyar Dalilin Da Yasa Aka Saki Murja Ibrahim Kunya Daga Gidan Yari
Murja Ibrahim Kunya 

Ba Alkali ne ya bayar da belin Murja Kunya ba, Cewar Kakakin Kotunan Shari’ar Musulunci


Mai magana da yawun kotunan shari’ar musulunci na jihar Kano Muzammil Ado Fagge, ya ce basu da masaniyar fitar da Murja Ibrahim Kunya, daga cikin gidan ajiya da gyaran hali.


Muzammil Ado Fagge ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da menama labarai a ranar Lahadi, ya ce a iya sanin su a zaman kotun makon da ya gabata, alkali ya aike da Murja gidan gyaran hali ne har zuwa ranar Talata 20 ga watan da muke ciki domin duba yiyuwar bayar da ita belin ko kuma akasin haka.


Ya kara da cewa a yadda suka sani har kawo yanzu Murja Kunya tana cikin gidan gyaran hali kamar yadda yake a shari’a, amma dai bai yi mamaki ba idan an ce an bayar da ita Beli.


Sai dai a zantawar gidan rediyon Dala FM Kano da mai magana da yawun gidan ajiya da gyaran hali na jihar Kano SC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, a ranar Lahadin nan ya ce, kamar yadda suka samu takardar ajiye Murja, haka suka samu takardar sakin ta hakan ya sa suka sallame ta amma dai ba guduwa ta yi ba.


Al’umma dai na ci gaba da bayyana albarkacin bakin su akan yadda akayi zargin jarumar Tik-Tok din tayi batan dabo daga cikin gidan ajiya da gyaran hali, bayan da babban kotun shari’ar muslunci dake zamanta a Gama ta aike da ita bayan da hukumar Hisbah ta Kano ta gurfanar da ita a gaban ta bisa zarginta da yada badala.


Shin wa kuke ganin yana da hannu kan sakin Murja Ibrahim Kunya? Kuna ganin za'a iya kawo karshen masu badala dake bata tarbiyyar matasa? Ku bayyana ra'ayoyin ku.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post