Hanyoyin Da Mata Za Su Kula Da Lafiyar Jikinsu A Lokaci Da Bayan Al'ada

Hanyoyin Da Mata Za Su Kula Da Lafiyar Jikinsu A Lokaci Da Bayan Al'ada
Hanyoyin Da Mata Za Su Kula Da Lafiyar Jikinsu A Lokaci Da Bayan Al'ada 


Tsaftar jiki ga mace a lokaci da bayan gama jinin al'ada wajibi ne, hakan zai sa jikinki ya kasance cikin tsafta da ban sha'awa Musamman ga mijinki 


Yakamata duk macen da tasan kanta bai kamata gidanta arasa wadannan abubuwan ba. Karki bari wai sai mijinki ya sayo miki. Yakamata da kanki ki gyara kanki sai dai maigida yajiki kin zama ta daban. Sai dai in baki iya ba tom, ina bawa maza shawara kar subar gidansu ba wadannan abubuwa. Suje su sayo su ajewa mata.


Sune kamar haka; farko ki ware flask


1. Karo

2. Kanunfari

3. Ganyen magarya

4. Ganyen lalle


Wadannan abubuwa sunada matukar gyara mace. Bawai sai lalle kin gama al'ada zakiyi amfani dasu ba, su zama kina amfani dasu akai-akai. Sannan kizama kinyi sallama dayin tsarki da ruwan sanyi kuma kinyi sallama da sawa gabanki sabulu, kikayi hakan shawarace, musamman sabulu mai chemical.


Wadannan abubuwan da muka lissafa su zama sune kayan tsarkinki. Misali kisami karonki ki sama sa ruwa kadan ki dafa shi sai yayi kauri, kidan lakata kadan ki shafa agabanki, Bayan kamar minti talatin sai ki dafa ganyen magarya da ganyen lalle da kanunfari kisaka gishiri kadan, sai ki kama ruwa dasu. Ki wanke ko ina agabanki. In kin samu dama sai ki hada kanunfari da muski kadan ki turara gabanki dasu. Hmm in kika saba da wannan bake ba ciwon sanyi, sannan bake ba karnin gaba ko warin gaba. Kuma mijinki bazaiyi complain ba dai-dai yake jinkiba. Ba sai nace komai ba da kanki zaki biyoni da takwicin addu'a ta musamman.


Kula da jiki Bayan Gama Jinin Al'ada 

Bayan kin gama jinin al'ada yanada kyau ki samu ganyen magarya da turaren miski, bayan kin gama wankan tsarki sai ki samu alimun (alif) da lemun tsami ki tafasa. Idan yasha iska sai ki wanke kowane lungu da sako na cikin gabanki. Domin yin amfani da alif da lemun tsami zai tsaftace miki gabanki ya wanke duk wani sauran datti dake gabanki. Kuma ya kashe miki kwayoyin cutar dake da akwai a gurin. Bayan wannan sai ki dauko ganyen magaryarki da kika tafasa, ki kara wanke kowane lungu da sako na cikin gabanki. Anan hikimar amfani da ganyen magarya shine, duk macen da take amfani dashi, babu wata macen da zata kaiki daraja a gurin mijinki, sai dai idan itama tana amfani da ganyen magaryar.


Ba dole sai kina jinin al'ada zakiyi amfani dashi ba. Bayan kin gama tsaftace gun da abubuwan da aka ambato a baya, sai ki dauko turaren miski ki rinka dangwalawa kina sanyawa agabanki.


Ki hada zaitun, miski, zuma guri guda ki shafa a gabanki. sai ki wanke. Wannan hadin yana magani kwarai game da warin gaba. Zai sa koda yaushe gabanki yarinka kamshi, kuma ya tsaftace miki gabanki.


Zaki iya hada ganyen magarya da kanunfari a guri guda ki rinka kama ruwa dasu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post