Abubuwan Dake Taimakawa Mace Samun Saurin Daukar Ciki

Abubuwan Dake Taimakawa Mace Samun Saurin Daukar Ciki
Abubuwan Dake Taimakawa Mace Samun Saurin Daukar Ciki 


Wannan darasi na matan aure ne musamman wadanda suke da juna biyu da wadanda ke shirin daukar juna biyu 

Ga matan auren dake son samun juna biyu, ga wata hanya da za ta taimaka muku don samun ciki cikin sauri. 


Ana samun furen dabino a daka shi, sai a samu lafiyayyar zuma a diba sai mace ta rinka matsi (insert) dashi, wato ta rinka matsawa a gabanta. Sannan kuma ta hada zuma ta rinka sha. Wannan hadin yana sawa mace ta gamsar da mijinta. Yana kuma wanke kowane irin datti da yake cikin gaban mace.


Haka kuma ga macen da takeson daukar ciki, wännan hadin yana taimakawa asamu ciki da sauri da yardar Allah.


(Ana samun furen dabino a islamic chemist).


Ga Macen Da Bata Son Ta Samu Ciki 

Sai ta samu ruwa lita daya tasha kafin saduwa da maigidanta. Bayan an gama ta kara shan ruwa tayi tsugunno tadan yi yunkuri kadan tayi fitsari.


Ga Mace Mai Ciki Amfanin Da Dabino Yake Mata Kafin Haihuwa Da Kuma Bayan Haihuwa 


Amfanin dabino a matsayin abinci ga mai ciki:

Yana kara karfafa jijiyoyin mahaifa, yana kuma taimakawa wajen saukin haihuwa. Yana kara takaita zubar jini lokacin haihuwa da bayan an haihu. Kuma yana baiwa mai jego koshin lafiya.


Yazo acikin kissar Maryam RA, inda Allah ya murce ta da cin dabino lokacin da take nakuda. Inda Allah SWT yace:

سورة مريم آية

25

وهزى إليك بجذع النخلة تسقط عليك رطبا جنيا"


"jijjiga katutturen dabino sannan zaki ga dabino sun fado nunannu. ki ci, sannan kuma ki sha, sannan ki samu nutsuwa". Suratu Maryam ayata 25.


Dabino yana dauke da sindarin potassium wanda yake taimakawa gudanyowar runan nono. Yawan tashin zuciya yana samuwa ne don rashin potassium. Dabino na magani, don yanada wani adadi mai yawa na potassium. Sinadarin iron dake cikin dabino na kara wanke jinin jiki. Yana rigakafin cutar anaemia. Dabino nada fa'ida ga jiki, domin ya samu sukari (glucose) wadatacce.


Guzirin mai juna biyu

Mai ciki zatayi amfani da wannan hadin:


1. Na'a-na'a

2. Kanunfari

3. Garin habbatus sauda


Sai a hadesu guri guda a tafasa a tace ruwan. A rinka sha Insha Allah za'a samu lafiya.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post