Abubuwan Dake Janyo Warin Gaban Mace

Abubuwan Dake Janyo Warin Gaban Mace
 Abubuwan Dake Janyo Warin Gaban Mace 

Amfani da ruwa mai sanyi, rashin tsafta na daga cikin abubuwan dake janyo warin gaban mace 

Warin gaba abune dake damun maza a lokacin da suka ji hakan daga matansu. Sai dai akwai abubuwan da yawa dake janyo gaban mace ya dinga wari. Hakan yasa muka kawo muku abubuwan dake janyo hakan da kuma yadda za ku magance matsalar hakan. 


1. Ya zamto a duk lokacin da bukatarta ta motsa ta kai kololuwa wurin sha'awa, takan sanya hannunta ko kuma tayi amfani da wani abinda zai sanya ta gamsu har ta kawo ma'ana ta biya bukatarta da kanta. Wannan shi ake kira a turance (masturbation). Hakan yana haifar da doyin gaban mace.


2. Macen aure da bata wanke gabanta bayan ta gama auratayya da mijinta. Tayi kwanciyarta akan cewa sai da safe ta hada tayi wankan tsarki. Hakan na sanya gaban mace yayi wari.


3. Barin wando (pant) yakai tsawon kwanaki uku a jikinki batareda kin wanke ba, yana daga abubuwan dake janyo warin gaban mace. Barin gashi ya taru a gaban mace, yana rike ruwan datti. Shima yana saka warin gaba.


4. Yin amfani da ruwan sanyi karara yayin da zakiyi tsarki. Na daga cikin abinda ke jawo warin gaban mace. Kin san dai wannan gurin yafi bukatar ruwan dumi. Inda son samu ne duk lokacin da zakiyi tsarki ki tanadi ruwan dumi.


5. Duk lokacin da zakiyi tsarkin bayan gida (kashi) ki hada shi da wannan wurin ki cakuda da sunan wankewa. Hakan kan sanya wari ko doyi ya samu wurin zama a gabanki.


6. Tafiya ba wando. Ya zamana ke sanya wando ba sabonki bane, kina iya zuwa ko ina ahaka batareda wando a jikinki ba. Wasu har unguwa suna fita ba tareda wando ba, daga 'yan matan har masu aure. Bayan kinada tabbacin a jikin mace ba inda yakai wannan jaha daraja da muhimmanci, amma sai mace ta rinka kunnen uwar shegu dashi.


7. Kokuma bayan kinyi wankan tsarki na al'ada, bazaki wanke gabanki da sabulu ba, bazaki yi amfani da miski domin gun yayi kamshi ya kori sauran tsami dake gurin.


Wannan sune abubuwan dake jawo Warin gaban mace, da fatan mata za su kiyaye da kulawa da gabansu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post