Yadda Ake Gane Alamomin budewar gaban mace - Android Pols

Yadda Ake Gane Alamomin budewar gaban mace
Yadda Ake Gane Alamomin budewar gaban mace


Alamomin budewar gaban mace 7 da ya dace kowace mace ta san su


Kamar yadda masana suka bayyana shi gaban mace tamkar roba yake, yana iya budewa kuma yana iya rufewa idan an rufe shi ta hanyar da ya kamata. Wasu matan basa kulawa wajen rufewa idan gaban su ya bude. Idan mijinki ya gane hakan za ki fita daga ransa a bangaren saduwa. 

Wasu matan basa sanin gaban su ya bude, hakan yasa muka kawo muku wasu alamomin budewar gaban mace domin ku yi kokari ku rufe shi ya koma tamkar na sabuwar budurwa. Ga jerin alamomin kamar haka;


Alamomin Budewar Gaban Mace 7

1. Mafi yawan mata masu fama da matsalar budewar gaba suna na fama da matsalar rashin riƙe fitsari, wato ɗigar fitsari. Digar fitsarin zata iya faruwa a lokacinda kika ɗauki wani abu mai nauyi, ko lokacin da kika yi dariya, tari, ko atishawa. Wannan alamace cewa mace nada budewar gaba.

Yawan shekaru, yawan haihuwa, yawan jima'i, tiyatar likita (ƙarin kofa) ko wani rauni a  gaban mace, ko tsayawar al'ada (menopause) saboda karancin sinadarin "estrogen" na iya sanya raunin tsokokin farji wanda daga ƙarshe zai iya haddasa buɗewar tsokokin bangon farji masu matse gaban mace.

2. Hanya ta biyu da zaki iya sanin ko kina da budewar gaba mai faɗi itace: ki saka ɗan yatsanki guda (manuni) cikin gabanki sa'annan kiyi ƙoƙarin matse dan yatsan da tsokokin farjinki. Idan har kin gwada yin hakan kuma ya zamanto baki iya jin kina matse dan yatsan da farji ba, to zai iya zama kina da babban wuri. Bugu da ƙari, idan kika saka yatsa 2 ko 3, misali manuninki da kuma yatsan tsakiyar hannnunki (mafi tsawo), kuma baki ji wata alamar bangon farjinki yana matse yatsun ba to alamomin budewar gaban mace ne. 

3. Idan ya zamanto yana da wuya kamin kiji ƙololuwar dadi (orgasm)/kawowa lokacin saduwa. Yana iya yiwuwa alamar budadden gaba ne. Haka kuma, raguwar jin dadi ba kamar daba shima na iya zama alamar.

4. Idan ya zamanto mace tana wasa da gabanta domin biyan buƙatarta kuma tafi sha'awar ta saka wani babban abu a gabanta akan ƙarami - wato bata jin dadin ƙaramin abu idan ta saka a farji sai babba. Shima alamace cewa mace nada girman farji. A baya munyi bayani da tsoratarwa akan wasa da gaba. Yana da illa ga lafiya da rayuwar auren 'ya mace. Don haka sai a kiyaye.

5. Idan ya zamanto kina shan wahala kamin ki gamsar da mai gidanki wajen jima'i ba kamar daba alamomin budewar gaban mace ne, sai ki tashi ki nemi magani don dawo da martabar ki.

6. Idan ya zamanto sai kin matse ko haɗe cinyoyin ki biyu sosai sa'annan kike jin dadin jima'i da maigidanki. Wannan ma yana iya zama alamar budadden gaba. Duk da dai cewa wani lokacin yana iya zamantowa mijin ne keda ƙaramar al'aura. Amma idan kamin haihuwarki babu wannan matsalar sai daga baya to sai ki zargi budewar gaba.

7. Idan ya zamanto kina jin ƙarar fitar iska daga farjinki lokacin da maigidanki yake saduwa dake, iskan kamar fitar "tusa" amma ba tusa bace (fanny farting) kuma babu wari. Iskan yana shiga yana fitowa  lokacinda maigida yake kaikawo. Wannan alamace kina da budadden farji.

Wannan sune wasu daga cikin alamomin budewar gaban mace 7 da ya dace kowace mace ta sani domin sanin irin halin da take ciki. Sannan a yi kokarin neman magani mai inganci wanda baida illa ga lafiyar mace. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

  1. shin Mai yake sawa daga mace in ana sadiwa ta dinga cewa bata jin mijinta Kuma bayan sun haihuuwar fari hàkan yake faruwa

    ReplyDelete
Previous Post Next Post