Don Matan Aure: hanyar zubar da ciki

hanyar zubar da ciki
hanyar zubar da ciki


Abubuwan da ke kawo zubewar ciki Zazzabin cizon sauro Magunguna(drugs) Incomplete service


ZUBAR DA CIKI (Abortion): Dalilai, matsaloli da hanyoyin kiyayewa: Zubar da ciki wanda a turance aka fi sani da abortion yana nufın zubar da ciki kafın lokacin haihuwa ya zo, wato kafın wata tara ya cika. Wannan zubewar cikin kuwa ya faru ne da niyya ko kuma wani dalili ne na daban ya kawo shi. Hanyar zubar da ciki (abortion) ya kasu kashi-kashi, ga su a takaice kamar haka: 


  • Incomplete abortion: Shi ne wanda ya fado amma akwai sauran wasu da suka rage. 
  • Theoretic abortion: Ana yin sa ne don ceton rayuwar uwa. Illegal abortion: Akasarin irin wannan abortion din 'yan mata kanyi shi, idan sun yi ciki kafın aure (wadda akafı sani da cikin shege). Akwai wanda cikin ke zuba lokaci-lokaci. 
  • Mist abortion: Cikin bai fado ba amma yana zuba.
  • Complete abortion: Cikin ya fado gaba daya a lokaci guda


Abubuwan da ke kawo zubewar ciki Zazzabin cizon sauro Magunguna(drugs) Incomplete service, shi ne wanda bakin mahaifansu ya ke a bude Kwayoyin cutar ciwon sanyi.


 Alamomin zubewar ciki

Idan ciki ya zube akwai wasu alamomin da mace za ta ji kamar haka:

  • Matsanancin ciwon mara
  • Jiri
  • Amai
  • Rashin jini
  • Rashin cin abinci. 

Hanyoyin magance zubewar ciki

Dakatar da zubar jini wanda aka gano bakin mahaifarsu budaddiyace akan dinka bakin mahaifar sai an ga cikin ya isa haihuwa sannan sai a kwance. Dakatawa da saduwa da iyali in cikin baida kwari, kuma in tana zubar da jini sosai da yawa za a yi mata karin jini. A kan ba da kwayoyin kashe ciwo (antibiotics and pain relever), da kuma cuta da na rage zafın maganin karin jini, da na cin abinci mai kyau. 


Riga kafı/kiyayewa Fara zuwa awo asibiti da wuri Kiyaye shan magunguna wanda ba likita ya rubuta ba, samun isashen hutu da daina daukar abubuwa masu nauyi: 


Matsalolin dake biyo baya bayan zubewar ciki: 

Masana sun bayyana illolin dake iya haifarwa ga mace idan an zubar da ciki sune kamar: Doguwar suma,

Mutuwa, 

Rashin haihuwa ga Wasu. 


Wadannan sune takaitattun bayanai da mu ka samu dangane da hanyar zubar da ciki. Don haka yana da kyau mu kula da iyalanmu masu juna biyu, sannan ga 'yan mata masu zubar da ciki su ma su sani akwai matsala babba dangane da hakan.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post