Manyan Alamomin HIV Na Zahiri

Manyan Alamomin HIV Na Zahiri
Manyan Alamomin HIV Na Zahiri 


Manyan Alamomin HIV Da Mutum Zai Iya Saurin Ganewa 


Manyan Alamomin Da Zaka Gane Kana Da Cutar HIV/AIDS (Cutar Mai Karya Garkuwar Jiki)


Ita dai wannan cuta wato (HIV AIDS) wata cuta ce wacce kwayar cutar virus ke haddasata ta hanyoyi daban daban. Ita dai wannan cuta tana matukar karya da kuma kassara garkuwar jikin dan adam (Immune system).


HIV/AID tana daya daga cikin cututtuka da mutane ke fama da ita kuma ba kasafai alamominta ke bayyana a jikin dan adam ba shiyasa ake kiranta da "Silent killer" a turance domin kuwa takan iya daukan shekaru goma ko fiye da haka kafın alamominta su fara bayyana a jikin dan Adam.


Cutar HIV/AID ba karamar sauran cuta ce ba, domin kuwa takan zama barazana ga garkuwar jiki (Immune syetem) Domin kuwa tana kassara garkuwa ta hanyar fafatawa da abinda ake kira CD4 a turance.


Bisa ga yanda alkaluma na hukumar lafıya ta duniya (WHO) ta wallafa, akwai kimanin mutane miliyan talatin da takwas da digo hudu (38.4 million) dake dauke da wannan cutar a fadin duniya, haka zalika kimanin mutun dubu dari shida da hamsin (650,000) suka rasa rayuwarsu sakamakon wannan cuta a shekara ta dubu biyu da ashirin da daya (2021).


Bayan haka kuma, bincike ya nuna mafi yawan wadanda ke dauke da wannan cuta ta HIV/AIDS a duniya shekarunsu basu gaza shekara ashirin zuwa talatin da biyar ba (20-35 years). Madogara (WHO). 


Shin Ta Wacce Hanya Ake Kamuwa Da Wannan Cuta, Kuma Menene Manyan Alamomin hiv


Yanada kyau duk wata cuta da ake bayanin ta, al'umma su san hanyoyin da ake iya kamuwa da ita, ita dai cutar HIV/AIDS ana kamuwa da itane ta hanyoyi wadanda suka shafi jini, maniyy ko kuma mama(breast) na shayarwa, bawai dole sai ta hanyar Jima'i ba. Ga kadan daga cikin Hanyoyin;


  1. Yin jima'i da abokan jima'in da suka wuce daya, 
  2. Yin jima'i ba tareda kariya ba (unprotected sex)
  3. Ta hanyar shayarwa (breast feeding)
  4. Lokacin Haihuwa (Delivery)
  5. Jima'i ta dubura (Anal sex)
  6. Jima'i ta baki (Oral sex)
  7. Lokacin karin jini (blood transfussion)
  8. Wajen Aski (barbing) idan har aka yi amfani da abin askin akan wanda yakeda cutar kuma abun askin ya sadu da jinin shi
  9. Wajen kitso(Idan ba'a tsabtace tsinke ba) Da dae sauransu.


Kadan Daga Cikin Hanyoyin Da Ba'a Daukar HIV/AIDS


  •  Cizon sauro (Mosquito) baya iya yadata
  • Sumbata (Kissing)
  •  Runguma (Hugging)
  •  Ba'a daukanta ta hanyar Fitsari
  • Zama a kusa da wanda keda ita
  • Tafiya tare a ciki mota
  • Cin abinci a tare
  •  Ta hanyar Gaisuwa (Hand Shaking)
  • Saka tufafın wanda ke dauke da ita da dai sauransu.


Da yawan masu wannan cuta suna rasa rayuwarsu ne sanadiyyar tsangwama da kyama da suke fuskanta a gurin al'umma, ya kamata musani cin abinci, yin labari ki kuma sanya tufafın wanda ke dauke da wannan cuta, baya shafuwar mu da komai, sannan musani wannan cutar, ba cuta ce wadda ake iya dauka ta kowace hanya ba, mu kula muyi mu'amala da masu wannan cuta mu'amala mai kyau wadda zata taimaka musu domin su samu sauki.


Manyan Alamomin HIV/AID Da Mutum Zai Gane 

Manyan alamonin wannan cuta sunada yawa, kuma alamomin sun danganta da wane irin mataki ko kuma tasiri ita wannan cuta tayiwa garkuwan jikin dan Adam, kadan daga cikinsu;

  1. Kuraje wadanda basa warkewa
  2.  Ciwon Gabbai
  3. Ramewa
  4.  Tari( Mai tsanani)
  5.  Ciwon Kai(Tsanani)
  6.  Yawan gajiya
  7.  Mutuwar jiki
  8.  Zawo da amai
  9. Masassara (Fever)


Ita dai wannan cutar har yanzu bincike bai tabbatar da sahihin maganin taba. Amma akwai magunguna wadanda ake kira (Anti-Viral medications) da ake amfani dasu domin rage zangon wannan cuta a cikin dan jikin dan Adam, da kuma wasu magunguna da ake kira Immune boosters wadanda suke kara karfin garkuwar jiki.


Cin abinci mai gina jiki, kula da tsabtar muhalli domin kare kai daga kananan cututtuka kamar su Malaria da Typhoid yana taimakawa gurin karin lafıyar wanda yake dauke da wannan cuta.


Shin Taya Zan Iya Kare Kaina Daga HIV/AIDS

Zan iya kare kaina daga wannan cuta kuwa??? Amsar itace Eh zaka iya, Ga kadan daga cikin hanyoyin da mutum zai bi domin kiyaye kanshi daga wannan cuta;

  • Bari yin jima'i bar ka tai
  • Yin HIV test kafin Aure
  • Yin Amfani da Kwararon roba lokacin Jima'i (Condom)
  • ka tabbatar an tsabatace "Clipper" kafın amaka aski
  • Ki tabbatar an tsabatace "tsinke" kafın amaki kitso
  • Barin yin amfani da reza wadda wani yayi amfani da ita Da dae sauransu.


Shawara Ga Wadanda Ke Dauke Da Wannan Cutar Ta HIV/AIDS


Kasani/Kisani cuta ba mutuwa bace kuma ba wanda ya isa ya kaucewa kaddararsa a duniya, kuma dan mutum yana dauke da wannan cutar ba shine zaisa mubar mu'amala dashi ba.


Kuma kamar yanda na ambata a baya ita wannan cukar ba'a daukar ta sai daya daga cikin hanyoyin cudanya da jini, maniyyi ko kuma mama(shayarwa) na shayar da yaro.


Idan ka/ki kasance daya daga cikin wadanda ke dauke da wannan cutar to ga shawara;

  1. Ka yawaita zuwa asibiti domin neman shawarar masana da kuma bin abinda suka gayama
  2. Yawan motsa jiki yanada amfani matuka
  3. Barin Shaye-shaye
  4. Barin damuwa (Stress & Depression)
  5. Cin abinci ingantacce (Balance Diet)
  6. Kada kayi kokarin yada wannan cutar


Allah yabamu lafıya kuma ya kare mu daga cututtukan zamani.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

  1. Masha Allah,Allah kakaremu daga duniya da lahira

    ReplyDelete
Previous Post Next Post