Manyan Alamomin Tashin Alkiyama

Manyan Alamomin Tashin Alkiyama

Manyan Alamomin Tashin Alkiyama


Yadda Ake Gane Manyan Alamomin Tashin Alkiyama


Wasu na ganin idan an yi maganar tashin alkiyama kamar wasa ne, sai dai babu wani batun wasa a ciki domin alkiyama gaskiya ce kuma kowa sai ya je. Hakan yasa a yau na tattaro muku wasu daga cikin jerin alamomin tashin alkiyama da ya kamata ku sani. Ga su kamar haka;


Manyan Alamomin Tashin Alkiyama

1. Aiko Annabi (sallallahu alaihi-wasallam) (ranar litinin, 21/Ramadan/0013bh daidai da 10/August/610m} yana shekara arba'in 40 da wata shida 6 da kwana goma sha biyu 12 lissafın wata/ shekara talatin da tara 39 wata uku 3 da kwana ishirin

2. Wafatin Manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) ranar litinin 12/rabi'ul-Auwal/11ah yana da shekara sittin da uku da kwana hu'du

3. Tsagewar wata

4. Karewar Sahabbai

5. Bude Baitil-Makdis.

6. Barkewar Annoba;- mai kama da ciwon dabbobi.

7. Bayyanar fitintunu masu yawa.

8. Bayyanar tashoshin tauraron 'Dan Adam.

9. Yakin Siffaini.

10. Bayyanar khawarij.

11. Masu da'awar Annabta ta karya

12. Yalwatar Arziki a doron kasa, Arzi'ki zai yalwata

13. Bayyanar wuta a Hijaz, dutse mai aman wuta.

14. Ya'ki da turkawa.

15. Bayyanar Azzalumai masu duka babu dalili.

16. Yawan zubar da jini da kashe-kashe

17. 'Dauke Amana;- ma su Amana zasuyi 'karanci. Alamomin tashin alkiyama ne. 

18. Koyi da Yahudu da Nasara.

19. Baiwa zata haifi uwargijiyar ta.

20. Bayyanar masu tsirara-tsirara (basa shiga ta addini)

21. Matsiya ta, Matasa masu kiwon awaki zasuyi yin dogayen gine-gine.

22. Yin Sallama ga wanda aka sani kawai;- mutane za su daina yiwa mutum Sallama sai sun sanshi.

23. Yaduwar kasuwanci;- ko ina zai zama kasuwa.

24. Mata zasuyi tarayya da mazansu a kasuwanci.

25. Wasu tsirarun 'yan kasuwa zasu mamaye kasuwanci;- ya zama ba ayi dakai sai da yardarsu.

26. Shaidar Zur.

27. 'Boye shaidar gaskiya.

28. Yawan Rowa;- mutane zasu zama marowata.

29. Yanke zumunta.

30. Munana makotaka

31. Yaduwar laifuffuka.

32. Bayyanar jahilci.

33. Amincewa maha'inci, da tuhumar mai Amana.

34. Mutuwar Mutanen 'kwarai da Ya'duwar lalatattu.

35. Yaki Halal Yaki Haram.

36. Rubda ciki akan Baitil-Mali (Asusun-gwamnati).

37. Mayar da dukiyar Amana ganimah.

38. Rashin fitar da Zakkah da dadin rai;- mutum ya ga zakka kamar Asara Ce yayi.

39. Yin Karatu dan Neman Abun duniya.

40. Yiwa mata biyayya da sabawa Uwa. 

41. Fifita Abokai ko Kawaye akan iyaye.

42. Hayaniya a masallatai.

43. Mafı yawan shuwagabannin Al'ummah zasu zama fasiqai.

44. 'Kas'kantattu zasu zama manyan gari.

45. Girmama mutum don tsoron sharrin sa.

46. Za'a halatta Zina.

47. Halatta Alhariri ga Maza (sa Alhariri ga maza haramun ne, amma za ayi zamanin da za'a halatta shi.

48. Ya'duwar Kayan maye. Shima alamomin tashin alkiyama ne

49. Ka'de ka'de da raye-raye zasu mamaye Al'ummah. 

50. Masifa da Bala'i zasu yawa Har mutum ya dinga fatan mutuwa.

51. Wani Zamani da mutum zai kwana Mumini yawuni kafiri;- saboda mafi yawan maganganu da aiyuka da basa kan Shari'ah.

52. 'Kawata Masallatai da yin gasar Hakan (kaji ana cewa Masallacin mu yafı naku kyau).

53. 'Kawata gidaje dayi musu kwalliya.

54. Yawan Saukar Kwarankwatsa da Aradu.

55. Yawan Rubuce-Rubuce;- Ya'duwar Rubutuce- Rubucemarasa amfani. (jaridu da mujallu, da littafai da internet) ba a tunanin amfanin rubutun kawai da an rubuta.

56. Wanda suka 'kware a roko da ziga, su suka fi samun kudi.

57. Za shagala da karanta wasu abubuwa a bar Al'qur'ani.

58. 'Karancin Malaman fiqhu da yawan Gardawa.

59. Neman Ilimi a wajen 'kananan mutane;- 'karamin Mutum wanda baya aiki da ilimin sa.

60. Yawan mutuwar bazata.

61. Shugabancin Wawaye (kuma suna ganin kansu wayaiyu).

62. Lokaci zai dinga sauri.

63. Banzaye zasu mamaye kafafan ya'da labarai;- Mutumin daba kowa ba, kuma bai zan komai ba, zai dinga magana kan abubuwan da suka shafı Al'ummah.

64. Madaukaki a duniya shine banza 'dan banza;- kaga ana ta rububin wani wanda baida amfanin komai saboda wani shirme da yake Misali;- 'Yan Bal da Mawaka.

65. Maida cikin masallatai Hanyoyi.

66. Sadakin Aure zaiyi tsada, sai kuma yazo yai araha.

67. Dawakai zasuyi tsada sai kuma suzo suyi araha.

68. Kasuwanci zaiyi sauki (ta yadda zaka sai Abu ko ka sayar daga dakin ka, batare da kaje ko ina ba) Misali;- yanar gizo

69. Kafıran duniya zasuyi taron dangi akan musulmi.

70. Mutane zasu dinga gudun limanci acikin Sallah (saboda ba cikakken Albashi).

71. Aukuwar Mafarkin Mumini (in Mumini yai mafarki sai Abu yafaru.

72. Yawan karya.

73. yawan gaba.

74. Girgizar 'kasa.

75. Yawan Mata.

76. 'Karancin Maza.

77. Aikata Sabo a fili.

78. Maida karatun Al'qur'ani hanyar Neman kudi.

79. 'Kiba, mutane zasuyi ta kiba maiyawa.

80. Bayyanar mutane masu yin shaida tun ba a tambaye suba.

81. Masu Bakance basa cikawa.

82. Masu 'karfi zasu danne raunana.

83. 'Rashin Hukunci da Alqur'ani.

84. Yawan rumawa da 'karancin larabawa.

85. Yaduwar kudi.

86. 'Kasa zata fitar da taskokinta.

87. Za a dinga shafe halittar wasu mutane suna komawa wata Halitta daban.

89. Tsagewar 'kasa, ta hadiye mutane.

90. Wasu kwarangwazai, duwatsun da ba aan suba zasu dinga fa'dowa mutane aka.

92. Yawan ambaliyar ruwa.

93. Ruwan 'bala'i;- wanda baya fidda shuka ko tsiro. 93.wata fitina zata 'barke tsakanin larabawa Har takusa 'karar dasu.

94. Bishiya zatayi magana don taimakawa musulmi.

95. Dutse zai magana don taimakawa musulmi.

96. Ya'kin Musulmi da Yahudu.

97. Kogin furat zai 'kafe, a hango Dutsen Gwal a ciki.

98. Zamanin da za a yiwa masu addini kallon ba wayayyu ba.

99. 'Kasashen larabawa zasu samu cigaba mai yawa. 

100.Bayyanar wata Babbar fitina da zata shafi kowa

101 Bayyanar bakar fitina gama gari sai ta shafi kowa.

102 masifu za suyi yawa birni da kauye.

103 Wani zamani zaizo sujjada daya tafi duniya da abinda yake cikin ta, saboda karancin masu ibada.

104 Rigima akan ganin wata, saboda wata zai kumbura, ya dinka fitowa babba.

105 za a dinga kaura ana komawa yankin Sham wato Syria.

106 Yakin duniya tsakanin musulmi da Rumawa (Turawa).

107 Zaa bude yankin Qusdunsuniyya, karo na biyu, bayan na zamanin daular Usmaniyya.

108 Zaa dena rabon gado, (masu karfi su cinye na kanana). Alamomin tashin kiyama ne

109 Zaa dena farin ciki da samun ganima (saboda wadata tayi yawa)

110 Zaa koma amfani da makamai na gargajiya, saboda na zamani zasu dena amfani.

111 Zaa raya baitul Maqdis, bayan karbo shi daga hannun yahudawa.

112 Mutane zasu kauracewa Madina, idan shagala tayi yawa.

113 Madina zata kore ashararai daga cikin ta, babu mai jin dadin zaman madina sai mumini.

114 Duwatsu zasu gushe daga gurinsu, saboda gine- gine naci gaba.

115 Wani mutum zai fito daga yankin Qahdan na larabawa kuma mutane zasu bishi.

116 Bayyanar wani mutum mai suna Jah, Jah.

117 Dabbobin dawa zasuyi magana irin ta mutane, kamar zaki da kura da makaman tansu.

118 Tsumagiya ma zatayi magana, (Bulala)

119 Hancin takalmi zaiyi magana.

120 Jikin mutum zaiyi magana (kamar cinyarsa) tabashi labarin abin da iyalansa suke aikayawa idan bayanan.

121 Alkiyama bazata tashiba sai anyi watsi da musulunci, ba karatu ba aiki.

122 Alkiyama bazata tashi ba sai an dauke Alkur'ani mai girma daga cikin takardu, da kirjin mahaddata,

123 Wata bataliyar mayaka zasu tunkari macca da niyar yaki, amma kasa zata hadiye su a hanya.

124 Zaa kauracewa zuwa aikin hajji.

125 Kabilar kuraishawa zasuyi kadan a duniya.

126 Rushe kaabah ta hannun wani mutum daga yankin Habasha.

127 Wata iska mai dadi zata dinka dauke ran muminai idan musifa tayi yawa.

128 Zaa dinka yin ginai- ginai masu tsawo a Масса.

129 Wasu tsinannun mutane, zasu dinka laantar magabata, (Annabawa).

130 Zaa sami kayan hawa na zamani, alamomin tashin kiyama ne

131 Bayyanar Ma'hadi,

132: Bayyanar Dujal (babban balain da ake jira).

133: Saukowar Annabi Isah.

134: Fitowar Yajuj da Majuj.

135 Girgizar kasa (manya manya sau uku a duniya).

136: Hayakin dazai rufe duniya baki daya.

137: Bayyanar wata dabba (amfadi kamaninta a hadisai).

138: Rana zata fito ta yamma.

139: Wata wuta zata fito takora mutane, zuwa filin Mahshar.


Wadannan sune, alamomi na tashin alkiyama. Kamar yadda suka zo a cikin hadisai Ingatattu, idan mun sami lokaci zamuyi sharhi Akansu Insha Allahu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post