Don Mata Dake Shirin Yin Aure: Falalar Auren Miji Nagari - Android Pols

Don Mata Dake Shirin Yin Aure: Falalar Auren Miji Nagari

Falalar Auren Miji Nagari 


Don Mata Dake Shirin Yin Aure: Falalar Auren Miji Nagari da ba duka mata ne suka sani ba 


Auren Namiji na gari na da muhimmanci a zamantakewar aure, idan mace ta samu auren miji nagari ta huce takaicin duniya. Miji Idan ya kasance nagari ne koda bai da ko kobo abin alfahari ne. 


Ga wasu alfanu da mace zata amfanu dasu idan Allah yayimata rabon Auren miji NAGARI


1 Idan mace ta auri miji nagari kuma ta aureshi saboda ALLAH toh zata kasance cikin farin ciki da walwalar gangar jiki da ruhi saboda zai zama mata jigo, bango, majingina ta yadda zai bata cikakkiyar kulawa saboda dama shi miji nagari ya iya kula gami da bawa mace hakkinta iya gwargwado. 

2 Duk macen da tayi gamdakatar da samun Namiji na gari a matsayin maigidanta tabbas Zata rayu cikin cikakkiyar nutsuwa saboda zai sadaukar da lokacinsa domin ya saurari dukkan damuwar ta don ya kwantar da hankalinta gami da samar da farin ciki agareta. 

3 Miji NAGARI Aurensa ribane kuma rabone saboda idan kina gidanshi in sha ALLAH zaiyi iyakar kokarinsa dan ganin cewa ya ciyar dake halal komai kankantarsa ya kuma gujewa kawomuku haramun komai yawansa. 

4 Yana daga cikin babban rabo game da auren miji nagari shine a cikin unguwa babu wanda ya isa ya yiwa ya'yanki gorin uba domin shi koda yaushe burinshi shine yaga ya'yanku sun yi tarbiya kuma sun zama yaran kirki wadanda musulunci da musulmi za suyi alfahari da samunsu. 

5 Auren Miji NAGARI kwanciyar hankaline ga dukkan macen da ta samu domin Shi mutunne wanda zai yi iyakar kokarinsa bisa taimakon Allah dan ganin bai tauye hakkin matarsa ba da yake kansa. 

6 Idan har kinason kiga yadda ake tausayawa mace ake tarairayar mace ake damuwa da damuwar mace toh wannan duk sai A wajen miji nagari. 

7 Daga karshe dai Shi namiji NAGARI baya auren mace domin wata Ni'imar duniya mai gushewa kamar Kyau, Nasaba, Kudi da sauransu. Yana auren mace ne Saboda ALLAH kadai domin shi yasan cewa yin aure domin ALLAH kadai shine zaisa aci riba da kuma amfanin sa. Dan haka shi damuwarshi shine kawai ki kasance mai addini da kyawawan dabi'u. Anan ne zakiga yadda yake matukar nuna so da kauna agareki hadi da nuna kishi akanki. 

Yan uwa mata masu Albarka kudage da Addu'a ku kuma kama kanku ku zama NAGARI domin samun irin wannan jajirtaccen namiji. Allah ya hada kowace mace tagari da miji nagari.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post