Domin Matan Aure: Alamomin Shigar Ciki

Domin Matan Aure: Alamomin Shigar Ciki
Alamomin Shigar Ciki


Alamomin Yadda Mace Zata Gane Shigar Ciki (samun juna biyu) 


Shin wadanne alamu mace zata ji ko ta gani ko ta iya ganewa idan tana dauke da sabon ciki ta yadda za ta gane tun kafin ta je asibiti?

Wannan tambaya ce da matan aure suka dade suna yi, sai dai ba suka cika samun amsa yadda ya kamata ba. Yau a wannan topic mun kawo muku cikakken bayani kan yadda mace zata gane tanada ciki. 

Ba kowace mace ce ta kwana da sanin cewa babban abinda ke kawo batan wata shine samun juna biyu ba. Bayan juna biyu kuma cuttukan shigar kwayoyin cuta mahaifa sune kan gaba wajen kawo batan wata (Rashin ganin period), ko rikicewar lissafin wata.


Sauran abubuwan dake kawo batan wata sun hada da;

  • Shayarwa, 
  • Yawan damuwa ko ciwon damuwa,
  • Rashin zama wuri daya ko 
  • Rashin samun hutu, kamar masu wasanni masu tsanani, 
  • Wasu lokuta ma har da shan wasu magunguna barkatai walau na asibiti ko na gida.


Alamomin Da Mace Zata Gane Tana Da Ciki

Shin wadanne alamu ne da mace mai juna biyu za ta ji ta tabbatar ciki ne?

A watannin farko mace zata yi batan wata, bayan yan satuttuka, sai ta fara samun wadannan sauyin kamar haka;

  • Tashin zuciya da sassafe har da amai a wasu lokuta, koda ma ba'a ci komai ba. 
  • Saurin gajiya, idan anyi wani dan aiki ko jin jiri (dizziness) idan an zo mikewa,
  • Zub da miyau,
  • Zazzabi,
  • Rashin son kamshin koda turare a wasu lokutan. 


Gwajin Shigar Ciki 

To a wanne lokaci ne ake so aje ayi gwajin samun ciki?

  • A tabbatar ta hanyar auna fitsari, Sannan sai ayi hoton ciki, idan ma cikin ne to ta hanyar hoton za'a tabbatar acikin mahaifa yake ba'a waje ba wato (ectopic pregnancy).
  • A watannin da ciki ya fara tsufa kuma, kamar ya kai wata 3, akan ga alamu kamar haka: 


Yadda Ake Gane Girman ciki

Yawan jin fitsari ko zaryar yin fitsari, saboda abin da ke ciki ya fara danne marar fitsari. 


  • A wasu akan samu ciwon baya, da
  • Ciwon kirji wato zafin kahon zuci ko kwarnafi saboda ‘acid’ din ciki na tasowa a kirji. 
  • Sai kuma a fara samun duhun fuska da fitowar zane a fatar ciki, da budewar hanci a wasu da kuma nauyi ko ciwon nonuwa. 


Ba dole bane kowace mace ta samu dukkan wadannan alamun ba, amma kusan rabin mata suna samun a kalla rabin wadannan alamun da muka yi bayani. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post