Nayi mamakin yadda mawaƙan Arewa suka juya min baya - 442Mawaƙi Mubarak Abdulkarim (442) yace yayi mamakin yadda mawaƙan Arewa suka juya masa baya a lokacin da iftila'i ya afka masa na dauri a Gidan Kurkukun Ƙasar Nijar, wasu ma na ganin kamar yanzu ya zama wani abin ƙyama a cikin al'umma. 


Mubarak ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da sashen Hausa na BBC a ranar Asabar, inda ya ce sun sha bakar wahala a Gidan Kurkukun nan, domin babu Abinci sai Talgen Tuwo, ko dai mutum ya zuba Sukari ya sha, ko kuma ya bari idan Talgen ya daskare, yaje ya karɓo Miya yaci, kuma wajen karɓo Miyar ma sai mutum mai ƙarfi. 


Hakazalika 442 yace tunda ya shiga wannan halin har ya fito, abokiyarsa Safara'u bata neme shi ba, shi yasa shima ya fita daga sabgar ta, domin ita ce a haƙƙu da ta nemi shi.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post