Yadda Wani Magidanci Ya Kashe Jaririyar Da Aka Haifa Masa Don Baya Son Haihuwar Mace
Wani magidanci ya kashe jaririyar da aka haifar Mads domin shi ba ya son haihuwar mace sai namiji.


Wani matashi dan shekara 28 mai suna Misbahu Salisu ya kashe jaririyarsa mai kwana daya a duniya da wani maganin kwari mai suna, saboda ya fi son jariri. 


Lamarin dai ya faru ne a garin Doka Baici da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano.


Hukumar tsaro ta sanar da kama Salisu ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a Kano ta hannun mataimakin kwamanda Janar na ayyuka, Dr Mujahid Aminudeen.


Aminudeen ya ce Salisu ya amsa cewa shi ne ya ba wa jaririyar maganin kwari, bayan ya shayar da  mahaifiyarta kwaya a shayi dauke da maganin barci.


Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce ya fi son ɗa namiji amma matarsa ​​ta haifi mace, wanda hakan ya sa ya kashe jaririn, cewar jami'in tsaron a cikin sanarwar da suka fitar.


Daga Jarida Tsuntsuwa

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post