Al'ajabi: Yadda Matashin 'Dan Sahu ya Maida Miliyoyin Kudi da ya Tsinta A Keke - Napep

 


Wani matashi dake tuka Babur din Adaidaita Sahu mai suna Auwalu Salisu Wanda aka fi Sani da Na Baba dake bayan tashar Yan Kaba,  ya dawo da wasu kudi  Mallakin Alhaji Ibrahim Barka Daga kasar Chadi da aka manta a babur dinsa ranar Alhamis din data gabata. 


 Kudaden dai an manta su wanda yawansu ya haura Naira miliyan goma sha biyu a cikin Adaidaita sahun da yake tukawa, bayan yaga kudin sai ya koma inda ya sauke fasinjan ko zai ganshi amma bai tarar dashi ba, sai ya kai kudaden wajen mahaifiyarsa ya gaya mata cewa manta kudaden akayi a Adaidaita dinsa, nan take mahaifiyarsa tace yaje ya gayawa Mahaifinsa inda nan take Mahaifin yaron yace su koma su sake dubawa ko zaa ga mai kudin, da baa gani ba sai suka ajiye kudin a gida, basu taba ko sisi ba duk da cewa jiya da kyar suka samu garin kwakin da suka ci a gidan nasu kamar yadda Mahaifin yaron ya fada.


Kudin akwai Saifa Milyan 10 da Dubu 130 sai kuma sama da Naira Milyan 2. Biiyo bayan jin sanarwar cigiyar kudin a tashar Arewa Radio 93.1. 


Daga karshe an bashi tukuichin tsintuwa har Naira Dubu 'Dari 400.


Daga Abdulmumin Abubakar Tsanyawa 

www.arewaradio.com

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post