Cin Amana: Fasto Ya Yiwa Matar Abokinsa Ciki Daga Daga Zama A Gisansu

 Maƙota da iyalai sun shiga tsananin mamaki yayin da wani mutumi mai suna Tubosun ya yi zargin cewa matarsa ta haifi cikin da abokinsa tun na yarinta ya ɗirka mata a jihar Ondo. Jaridar The Nation ta rawaito cewa matar, wacce ta haifi yara uku tare da Tubosun tun bayan aurensu, ta ƙara haihuwa amma wannan karon ɗan na abokinsa ne wani Malamin Coci. 


Asirinsu ya fasu ne yayin da yayan magidancin, Moses Akinnuoy, ya kai ƙarar Malamin mai suna, Fasto Oluwaseun Akinnubi, kan abubuwan da yake yi a gidansu da ke layin a ƙaramar hukumar Odigbo, jihar Ondo. Fasto Akinnubi ya maida Falon gidan abokinsa (Mijin matar) zuwa coci inda ya ke gudanar da hidimar ceto ga mutane mabiya addinin Kirista da sunan gidauniyar Kiristoci. 


Yadda magidanci ya ba Malamin wurin zama Rahoto ya nuna tun asali mijin matar ne ya ɗauko Malamin cocin ya ba shi matsuguni a gidansu saboda lokacin ya rasa wurin zama. Majiyoyi sun bayyana cewa lokacin zamansa da ma'auratan ne ya lallaɓa ya ɗirka wa matar abokin nasa wanda ya ba shi wurin zama, ciki. Wasu bayanai sun nuna cewa Malamin ya taɓa faɗa wa abokinsa cewa Allah ya tsara cewa matar zata zama matarsa, kamar yadda rahotanni suka tattaro. 


Wata majiya ta ce: "Bayan ya yi wa matar ciki, sai ya kama hayar wani gida kuma ya ɗauke matar daga gidan mijinta ta koma inda yake zama." "Abun takaicin da maƙotan suka gani shi ne, bayan Mama Precious ta haifa wa faston ɗa, sai aka ga mijin yana zuwa gidan Faston yana wanke kayan matarsa da na jaririn." "Ɗaya daga cikin makotan ya kira mutumin ya ankarar da shi cewa Malamin ya kwace masa mata, amma ya nuna bai damu ba, daga nan suka gane ba ya cikin hankalinsa." 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post