Tsohuwar Jarumar Kannywood Safarau ta wallafa hotunan bikin zagayowar shekarar da aka haifeta a shafin ta na Instagram.
Masoya da dama sun tayata murna tare da tura mata fatan sakonnin fatan alheri.
Tun bayan barinta harkar fim jarumar ta koma yin wakoki tare da abokinta 442 wanda yanzu ake zargin ya mutu a kasar Nijar bayan kamashi da jami'an kasar suka yi sakamakon saba dokar kasar.
A baya-bayan nan cikin wata hira da aka yi da Safarau ta bayyana nadamar ta kan abubuwan da ta yi lokacin da take yin wakokinta.
Ga dai hotunan jarumar na bikin shekarar haihuwar ta.