Wannan mutumi ya kashe zaki a gabashin Afirka, inda ya samu raunuka da dama bayan ya yi fada da zakin na tsawon mintuna 90 don kare iyalansa.
Hotunan dake da ban tsoro sun fito daga kasar Uganda bayan da rahotanni suka ce wani mutum ya kashe zaki da hannunsa a wasan kokawa da aka yi wanda yai sanadin zubar jini mai yawa daga jikin mutumin wanda za ku ga duk jikinsa daure da bandeji.
Shafin Daily Star ta rawaito cewa mazauna yankin da mutumin ya fito sun tabbatar da faruwar al'amarin inda suka ce zakin ya yi kokarin shiga gidan mutumin inda suka fara yin kokawa da mutumin.
An dauki hoton mutumin cike da raunuka a jikinsa duk an yi masa liki da bandeji kamar yadda kuke gani cikin wannan hoton wanda zai iya daukar tsawon lokaci kafin ya warke.
Mutane da yawa ne ke ta cece-ku-ce a kan yadda mutumin ya nuna jarumtarsa su ka yi kokawa da zaki har ya kashe shi.
Lamarin dai ya faru ne a gundumar Mpefu Kagadi na kasar Uganda.
Shin za ku iya yin abinda wannan mutumin yai don kare iyalansa? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku.