Hatsarin Dake Tattare Da Masu Yin Amfani Da GBWhatsApp - Android PolsWasu mutanen suna da taurin kai sosai, tun tsawon lokaci ana fadamuku illolin dake tattare da yin amfani da manhajar GBWhatsApp amma basuji ba. 


GBWhatsApp 'mod' ne, don yanzu bai ba ka matsala ba, zai iya ba ka a gaba. A kullum sai na karɓi ƙorafi a waya ko chat kan 'banning'. Idan ka dama, ka cire, idan ka dama ka ci gana da amfani da shi, kai ta shafa.


Ba wani masanin fasahar zamani a sarrafawa ko ƙirƙirar 'saftwaya' da zai baka shawarar ka yi amfani da GBWhatsapp da ire-iren 'moded apps' saboda suna da hatsari ga waya da kuma bayanan cikin waya.


Idan ba ka yarda da bayanan ire-irena da muke ƙoƙarin wayar da kan mutane don kare kansu daga kutse, satar bayanai da abin dake lahanta musu bayanan waya, ka yi search a 'Google', is GBWhatsApp safe? Watakila za ka fi yarda da bayanan masu fararen kunnunwa. Ko lokacin da za ka ɗora a wayarka, na tabbatar wayarka ta maka 'warning', 'this app is not safe!'.


Don me za kana amfani da GBWhatsapp, ko FMWhatsApp, Aero, YoWa, Fouad, RC, Delta, OG, Plus, Soul... wasu ma ba ka sansu ba ko? Don:


• Saving status? Xender da Phoenix Browser suna yi.

• Hide view status? Normal WhatsApp da WABusiness suna yi. Ka shiga: Settings > Account > Privacy > 'Read Receipts' > Off.

• Last seen? Normal WhatsApp da WABusiness suna yi, shiga Setting > Privacy.

• Anti delete chat da status? Munafurci ne wannan.

• WhatsApp lock? WhatsApp ma yana yi.

• Boye chatting? WhatsApp ma yana da 'archive' 


Da zarar ka ce min WhatsApp ɗinka ya sami matsala, na tambeya ka, GB ko wani 'modded' ne? Ka ce, "eh!", zan ce ma calama! Tunda ba ka ji.


✍️Aliyu M. Ahmad

23th Dhul-Qadah, 1444AH

12th June, 2023CE


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post