Tinubu ya sanya hannu a kan dokar baiwa ɗalibai bashi a Nijeriya - Android Pols




Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu ta ƙasa.


Mai magana da yawun Gwamnatin Tarayya, Dele Alake ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar yau Litinin.


Sanarwar ta ce za a ajiye kuɗaɗen da za a rinƙa bayar da bashin ne a asusun Ma'aikatar Ilimi, kuma ɗaliban manyan makarantu ne kawai za su iya cin gajiyarsu.


Mako biyu da suka gabata ne ƙudirin, wanda shugaban Majalisar Wakilan Tarayya, Femi Gbajabiamila ya gabatar, ya tsallake karatu na uku a Majalisar Dokokin Tarayya.


Dokar za ta bai wa ɗalibai ƴan asalin Najeriya damar karɓar bashi cikin sauƙi, wanda babu ruwa a tattare da shi daga Asusun Bayar da Bashin Karatu na Najeriya.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post