Maza Gareku: Kuskure Ne Yiwa Mace Wadannan Abubuwan - Android Pols
Akwai wasu dabi'u da halaye na wasu mazan da suke cutar da mata dasu. Wasu mazan kuwa suke zubarwa kansu mutunci dasu. Akwai mazan da suke rasa soyayyar da ake yi musu saboda su.


Duk namijin da yake son yayi kyakyawan mu'amala da mace musamman wacce yake nema da aure ko wacce ya aura. To ka guji yiwa mata wadannan abubuwan kamar haka:


1: Kada Ka Furtawa Mace Kalmar So Bada gaske kake ba.


2: Duk Munin Mace Kada Kace Mata Mummunace Ita.


3: Kada Ka Sake Ka Kwatanta Mace Da Wata Muddin Ba Cewa Zakayi Ta Fita Da Wani Abun Ba.


4: Kada Ka Dakawa Mace Tsawa.


5: Kada Ka Sake Ka Tona Wani Sirrin Da Mace Ta Baka Ko Ta Fadamaka.


6: Kada Ka Yiwa Mace Alkawarin Da Bazaka Cika Ba.


7: Kada Ka Ci Amanarta Musamman Da Wata Na Kusa Da Ita.


8: Kada Ka Gwaleta A Cikin Mutane Ko yi Mata Gyara Na Kaskanci.


9: Kada ka Cutar Da Ita Saboda Soyayyar Da take yi Maka.


10: Kada Ka Zama Mai Tsautsauran Ra'ayi Ko Akida Akanta.


Mace idan tana yinka, tana yinka ne gaba dayanta jini da tsoka. Ranta da mutuwa. Don haka amfani da wannan nakasar kada ya baka damar ka cutar da ita. 


Kada ka sake kayiwa macen da take sonka abunda ba za ka so a yiwa ta kusa da kai ba. Mata Mutanen Mu.


Da fatan maza za ku dauki darasi daga wannan abubuwan da kuma Karanta, kuma da fatan za ku Kula sosai da zamantakewar ku da mata. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post