Zuwa Ga Maza Da Mata Masu Fama Da Sha'awa - Android PolsSamari da 'yan mata zawarawa har da matan Aure wannan shirin naku ne, da fatan za ku amfana daga cikin abubuwan da za ku karanta. 


Ya Allah kabawa wanda ya samu halin Karanta wannan rubutu ikon yin sharing zuwa ga sauran al'umma domin su amfana.


Samari da yan' mata suna yawan turawa malamai tambayoyi iri daban-daban akan yadda suke fama da tsananin sha'awa.


Wasu daga ciki sukan ce suna istimna'i wato yin wasa da al'aura wai don su gujewa aikata zina, bayan zinar suke aikatawa.


Istimna'i (wasa da al’aura) ya haramtu ta kowace irin siga kuma yinsa zai jawo azaba da ukuba ranar alkiyama matukar dai mai aikatawa bai tuba ya daina ba.


Fitar da maniyyi ta kowace irin siga haramun ne sai dai ta hanyar aure kawai.


Akwai Bala'o'i masu tarin yawa dangane ta masu wasa da al'aura.


Idan ka" kasance ko kin kasance kina fama da matsananciyar sha'awa kuma babu halin yin aure to akwai hanyoyi masu tarin yawa da zaku bi don gujewa fadawa tarkon shaidan.


Ga wasu daga cikin jerin hanyoyin kamar haka:


• Ku guji zama a daki ku kadai, ba tare da mutun yana wani aikin da zai ja hankalin sa ba.


• Ku guji yawan sanya sha'awar jima'i a cikin ran ku.


• Kuyi iya kokarin da za kuyi wajen kawar da kai daga shafukan da suke yada hotuna masu nuna tsiraici.


• Yawan yin azumin nafila yana mutukar taimakawa wajen nesanta mutum daga wannan dabi'a.


• Ka daina yiwa kowace irin mace kallon sha'awa, haka kema ki daina yiwa kowane irin namiji kallon sha'awa.


Mutum zai iya rayuwa cikin koshin lafiya ba tare da yana fitar da maniyyi ba har zuwa lokacin da zai yi aure, muddin dai mutun yana tunawa da azabar da Allah ya tanada ga  wadanda suka kasa rike sha'awar su.


Sha'awa irin ta samari da yan mata daga shaidan take, domin tana daya daga cikin manyan tarkunan sa da yake halakar da mutane dasu.


Amma dukkanin wanda ya ji tsoran tsayuwa da ubangijinsa ya hana zuciyarsa abin da take so daga sha’awa da istimna’i lallai aljanna ita ce makomarsa matsuguninsa da izinin Allah madaukaki


Rubutawa batayi mana wahala ba muna fatan sharing zuwa groups bazai yimuku wahala ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post