Kada Ka Furtawa Mace Kalmar So Har Sai Ka Fahimci Wadannan Abubuwan Daga Wajenta - Android Pols
Wasu mazan sukan dauka da zaran mace na yi maka faranfaran sonka take yi. Haka ne, amma ba duk faranfaran ne na soyayyar ba.


Don haka kada ka sake ka furtawa mace Kalmar kana sonta idan kuna da kusanci har sai ka fahimci wadannan abubuwan tukun.

 

1: Kayi kokarin gano ko ita ma tana da ra'ayinka. Ka binciko wannan gaisuwa, ladabi da girmamawan da take yi maka ita ma tana ra'ayinka ne. Da zaran ka samu tabbacin hakan daga buncikenka. To daga nan kana iya daukan mataki na gaba.


2: Idan ka gano tana ra'ayinka, kada kai tsaye ka nuna mata kana sonta har sai ka dubi yanayin da lokacin da ya dace. 


Kada kace za a yi amfanin da lokacin da ake wani hidima na buki ko bacin rai.


Kayi amfani da wasu ranaku na musamman ko kuma a duk lokacin da ka fahimci tana cikin walwala da jin dadi a tare da ita yadda zaka dace da amsarta.


3: Karkayi gaggawar furtawa mace kalmar so bayan kasan tanada wanda take soyayya dashi. Idan ka fahimci shi ke sonta ko ita ke sonshi wannan damace na furta mata duk kuwa ba lalle bane ta amince amma zaka barta da masaniyar tana gefe ko da ta baci. Amma idan soyayya suke yi, kaja bakinka kayi shuru ka danne zuciyar ka.


4: Kamin ka furtawa mace kalmar so ka tabbatar ka san abunda kalmar ke nufi Kuma a shirye kake zaka ki yaye. Kada ka furta mata kalmar domin cutar da ita. 


5: Kada ka zama ma gajen hakuri. Dole sai ka kasance mai hakuri kabi al'amarin a nitse kafin ka samu yanayi da hanyoyin furta mata hakan. Idan kace za ka yi sauri ko gaggawa wajen sanar da ita baka bi matakai ba, saurin naka zai zama na banza.


Bin wadannan matakan ya zamemaka dole ne saboda macece da ta sanka kasanta.

Da fatan za a kula.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post