Tarihin Masallaci Na Farko A Kasar Yarbawa - Android Pols



An gina masallaci na farko a kasar Yarbawa ne a garin Iwo da ke Jihar Osun a 1655, shekara 368 da suka gabata a yayin da aka gina masallaci na biyu a garin Iseyin a Jihar Oyo a 1760, sai garin Legas ya biyo baya a 1774 da garin Saki a 1790 da kuma garin Osogbo a 1889.


Garuruwan Oyo da Ibadan da Abeokuta da Ijebu-Ode da Ikirun da Ede sun biyo baya ne a cikin Karni na 18, yayin da Shehu Usman Dan Fodiyo ya kai jihadi zuwa garin Iwo.


Sarkin da ya fara gina masallacin mai suna Oba Ogunmakinde Ande ya musulunta ne kafin ya gina masallacin. Ya musulunta ne a dalilin rashin haihuwar ’ya’yan da za su gaje shi, inda ya nemi babban matsafinsa ya gano dalilin da ya hana shi haihuwar.


Bokan ya shaida wa Sarkin cewa, idan yana son haihuwa, to sai ya nemo irin mutanen nan masu wanke hannaye da fuska da kafafu (Musulmi) ya zauna tare da su.


Bai bata lokaci ba ya umarci fadawansa su kawo masa irin wadannan mutane. Lokacin da fadawan suka shiga gari sun hadu da Musulmi ’yan kasar Mali da ’yan Arewacin Najeriya masu fataucin kaya zuwa garin Iwo suka shaida masu umarnin Sarki yana son ganinsu.”



A ganawarsu da Sarki sun gaya masa cewa, idan har ya karbi addinin Musulunci to, zai samu haihuwa da yardar Allah.


Nan take ya amince ya karbi addinin Musulunci inda ya samu haihuwa cikin kankanin lokaci.


A matsayinsa na Sarki sai ya yi amfani da karfin mulkinsa ya gina wannan katafaren masallaci a kusa da fadarsa kuma shi da kansa ya zama limamin da yake jagorantar Musulmi yin salloli biyar a kowace rana.


Wannan masallaci shi ne na farko da aka fara ginawa a Kasar Yarbawa. Hakan ya nuna ke nan Masarautar Iwo ce, ta fara jagorantar masarautun Yarbawa wajen karbar addinin Musulunci tun kafin Shehu Usma Dan Fodiyo ya kawo jihadi zuwa masarautar a wancan lokaci.


Bayan rasuwar Oba Ogunmakinde dukkan sarakunan da suka biyo bayan Oba Ogunmakinde Musulmi ne, ba a taba nada Sarki mabiyin wani addini da ba Musulunci ba.


Sai dai Ance akwai wani sarki mai suna Abimbola da ya hau karaga a matsayin Musulmi, amma ya yi ridda ya koma wani addini.



Ance daga lokacin da ya yi ridda a kan karaga sai ya makance, ba ya gani da idanuwansa biyu kuma ya rika samun matsalolin da suka hana shi zama lafiya har zuwa lokacin mutuwarsa.


A Masarautar Iwo kadai ce ake nada wa sabon Sarki rawani domin tabbatar da karbuwar addinin Musulunci sabanin hula da ganye da ake nada wa sabon Sarki a sauran masarautun Yarbawa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post