kalmomin Soyayya Da Kauna A Zamantakewar Masoya - Android Pols




Idan kina so mijinki ya kaunace ki sai kin iya kalmomin kauna da soyayya ana so ya zamana kin san kalmar da zaki fadi ga ma maigida, kalmar da za ta kara jefa kaunar ki da soyayyarki a zuciyar sa, ki rika nuna masa irin soyayya da kaunar da kike yi masa ita zata zamo sinadarin kauna da soyayyarki a zuciyar sa wannan a dole sai kin koya


A sami wani lokaci idan za kiyi masa magana ki kirashi da wani suna na soyayya zaki iya kiranshi da wadannan sunayen kamar haka:

sweet heart

honey

masoyina

sahibina


Ko dai wasu kalmomin da za su faranta masa rai wata kalmar idan kin fada masa in yana jin nishadi to zai yi maki abun da zaki dade kina alfahari da shi. Yana da kyau mata su yi koyi da Nana Aisha matar ma'aiki lokacin da manzon Allah (S.A.W) ya bata labarin ummu zarrin yanda mijinta yake sonta yake kaunarta yake kyautata mata da ya gaya mata sai yace ai a gurinki kamar ummu zarrin ne da abu zarri.


Aisha tana daga kai ta kalle shi tace ya manzon Allah (S.A.W) ana maganar ka kuma wanene abu zarrin? Kafi alkhari fiye da abu zarri ga ummu zarri a gurina ya Rasulillah wannan kalma ce ta kauna da nuna soyayya. 


Ana so dole ki san yadda zaki nuna wa mijinki kauna da soyayya wannan yana daga cikin abunda yake kara dankon kauna da soyayya a cikin zaman aure.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post