Ga Wasu Hanyoyi 15 Da Namiji Zai Mallake Matarsa Cikin Sauki - Android PolsJigo na samar da al'umma da kuma jin kanta zai bi wajen samar da dawwamammiyar soyayya da kauna a tsakaninsa da matarsa. 


Da yake mata kamar yadda muka sani, wani irin kayan karau ne da yake bukatar kulawa ta musamman don samar da natija da kuma

jin dadin zama da ita.


Ya ishe mu misali kan raunin mace, domin ita da kashin hakarkari aka yi ta, idan ka matsa masa don ya mike sai ya karye, in kuma ka bar shi sai ya ci gaba da zama a karkace.


Don haka wajibi ne ya zama muna da ilimin zama da su. Akwai wasu hanyoyi da ya kamata mu sani don mu san yadda ya kamata mu zauna da su. Ga su kamar haka :


1. ka zamo mai tausasa zance a gare ta, kar ka zamo mai yawan fada


2. Idan ka shiga gida ka ce 'assalamu alaikum' sallam tana korar shaidan daga gida.


 3. Annabi (s.a.w) ya ce mata kamar kayan karau ne, saboda haka kula da su sosai, ka tuna akwai alkhairi a cikinsu, saboda haka sai a tarairaye su.


4. Idan za ka ba ta shawara ko za ka yi mata fada ya zamo a cikin sirri, wato a lokacin da kuke ku kadai, kada ya zamo a cikin mutane, don yin hakan muzantawa ne.


5. ka zama mai kyautatawa matar ka, hakan ya na kara soyayya.


6. Idan ta zo za ta zauna ka tashi ka ba ta wurin zamanka, hakan zai tausasa zuciyarta.


7. ka guji yin fushi ta hanyar rike alwala a ko da yaushe. Annabin rahma (S.A.W ) ya ce: idan ka yi fushi, to idan a tsaye kake sai ka zauna, idan a zaune kake sai ka kwanta.


8. ka rinka yin ado kana sa turare saboda ita.


9. kar ka zamo mai tauri (mai mako) Annabi (S.A.W ) yace "ni ne mafi kyautatawa zuwa ga iyalina" idan ka yi tauri da yawa ba za ka 

samu kusanci zuwa ga Allah ba. Haka kuma ba za ka zamo namiji jarumi ba.


10. ka dinga sauraron duk abin da matarka za ta gaya maka ko da kana ganin abin ba shi da muhimmanci, hakan zai sa ta san ka damu

da ita.


11. ka kaucewa yin musu da matarka, yin haka yana kawo rabuwar kai.


12. Annabi (S.A.W ) ya ce ku kira matanku da sunaye masu dadi, sunan da suke so su ji ka kira su da shi, Misali:


my one

my heart

my love

my princess my my my my da sauransu. 


12. ka rika yi mata tsarabar ba zata, idan tana sha'awar wani abin marmari sai ka sayo mata ba tare da ta sani ba.


13. ka kula da harshenka zuwa gare ta, wato ka guji abubuwan da za su sa ta yi fushi.


14. Mutum tara yake bai cika goma ba, ka yi hakuri da duk wani aibin da take da shi sai Allah (SWT) yasa albarka a cikin aure naku.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post