Idan Kina Son Kaucewa Wulakanci Namiji A Soyayya Guji Yin Wadannan Abubuwan - Android Pols
Na sha fadi, kashi 80 na matan da suke kukan maza sun yaudaresu da zaka zauna ta baka labarin yadda aka yi sai ka fahimci laifinta ne.


Duk kuwa da akwai wasu halayen mata da dabi’un su da su kansu ba za su iya kauce musu ba sai wacce Allah Ya kare. Sai dai kina Iya amfani da hankalin da Allah SWT Ya baki domin amfanar kanki da kanki.


Ga wasu abubuwan da za ki kauce su muddin baki son nan gaba ki soma kukan an yaudareki.

 

1: Kada ki matsawa saurayi ko duk wani namiji da ya nuna miki soyayya. Matsawa irin na yawan kira da tura sakonnin text a farko farkon soma soyayyar ku.


Daure ki rabu dashi. Idan ya kiraki ki dauka, kuma kada ki nuna masa rashin kiranki da baiyi ba ko ba yayi da wuri yana damunki. Kuma kada ki bari hakan din ya dameki.


2: Ki guji neman yin kusanci da shi yadda za ki manne masa ko makalemasa.


Nunawa namiji wannan mannau din da yawan shiga duk inda yace ku shiga zai iya zamemiki illa a nan gaba.


A kullum kada ki nunawa saurayi soyayyar da kike yi masa zai iya sa ki bishi duk inda yake bukatar ki bishi ko ki shiga da shi.

 

3: A kullum yi kokarin nuna masa bafa shi kadai ke sonki ba, ba kuma sai da shi zaki iya rayuwa ba.


Ki rika kokarin cusa masa shakku a zuciyarki na ko baki sonshi ne. 


4: Kada ki zama mai neman wani abu daga gareshi. Kada ki sake ki nuna masa talauci da gazawarki domin ya baki kudi ko taimaka miki.


5: Kada ki kauda kai ko yin shiru akan duk wani abu da yai miki ko ya furta miki da baki ji dadin abun ba. Nuna masa rashin dacewar hakan, da kuma fatan zai kiyaye nan gaba.

 

Nemawa kanki mutunci a wajen namijin da yake sonki da aure tun a farko-farkon soyayya ake yin hakan ba sai kun zama jiki ba.


Da zaran kin yi sakaci da wasu abubuwan a tun farko, ke abun zai wahalar a nan gaba.


Da fatan mata musamman 'yan mata zaku kiyaye.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post