Hanyoyin Magance Istimna'i Da Illolin Da Suke Haifarwa - Android PolsKamar dai yadda na wallafa a kwanakin baya inda na zaiyano illolin da yawan Istimana'i kan haifar ga jikin namiji wanda a wannan karon ba bukatar in sake yin magana akan matsalar sai dai bayani akan hanyoyin da za'a bi dan samun waraka ga matsalolin da wannan dabi'a ta masturbation take haddasawa musamman ganin irin yawan sakonnin da nake samu ta bukatar hakan daga Mabiyansa mu.


Idan dai har yin istimna'i ya haifar maka da daya ko fiye da haka daga cikin wadannan matsalolin da zan zaiyana to akwai bukatar ka bi wadannan hanyoyin dan samun waraka.


1.Saurin inzali.(Premature ejaculation)


2.Rashin karfin zakari.(soft and weak erection)


3.Digowar maniyi a yayin fitsari ko bayan gari(semen leakage)


4.Low libido (karancin sha'awa 

) kai za ka ji tamkar baka balaga ba. Baka da wata doguwar sha'awa a jiki.


5.Tsananin kasala (fatique)


6.Saurin manta abu ko rike karatu (forgetfulness and lack of confidence)


7.Saurin kwanciyar zakari (short term erection)nan take zakari da ya tashi baya jimawa sai ya sake kwantawa.


8.Bayan gari mai tauri (constipation)


9.Kankancewar gaba (smallness of penis) kaikace na karamin yaro ne.


10.Rashin ruwan maniyi masu kauri (thin semen fluid)


Mataki na farko anan shi ne ka canza tsarin rayuwarka gabaki daya waton life style.


Ka nisanci duk wani abu da zai saka yin istimna'i. Magangannun batsane kall-kallen hotunan fitsara da dai makamantansu.


Mataki na biyu : Ka rika cin abinci mai gina jiki (balancediet). A hakika abinci na daya daga cikin manya-manyan abubuwa masu taka rawa ta musamman dan samar da jini da maniyyi ga jikin dan adam.


Dan haka a rika cin abinci mai dauke da sinadirran dake da alfano ga jiki, kama daga sinadiran dake inganta lafiyar koda, zuciya da kwakwalwa gami da na lafiyar mazakutar namiji(reproductive system)


Abinci da dama da muke ci muna ci ne kawai dan maganin yunwa amma a hakikanin gaskiya ba wata martaba yake yiwa jiki ba, baya dauke da nutritional values din da jiki ke bukata, sai kaga anci abinci amma ana ta faman zuwa toilet saboda baya da wani amfani ga jiki.


Ba wai sai abinci mai tsada ke da vitamins ba, da dama muna ganin kamar sai mai hali ke iya cin abinci mai sinadiran dake gina jiki; wannan ba haka bane. Misali ga su zogale wallahi ba karamin taimakawa jiki ya ke yi ba.


Ga su ganyen alaiyafu da wake a rika dafawa ana ci.


Ga kwai dafaffe duka kwaya daya zuwa biyu ya wadatar ba abinci bane da za'a zauna a yiwa cin tuwo ba, abinda ake bukata kawai a rinka ci akai-akai amma bada yawa ba, dan shi abinci nau'in protein ba ya bukatar a ci shi da yawa yana iya haifar da gudawa ko lalacewar ciki. 


Kamar dangin kwai(eggs) meat (nama), madara(milk), kifi (fish), beans(wake).


Mataki na uku a rika shan yan itatuwa fiye da abincin da kake ci: Dalili anan jikinka ya rasa wasu muhimman sinadirai wadanda suna nan a cikin maniyin da kake ta zubarwa akai-akai, wanda 'yayan itatuwan kawai za su taimaka maka ka samu damar dawowa da wadannan sinadiran da ka rasa.


Haka kuma cutukka da dama da basa jin magani ana warkardasu ta yawan shan yayan itatuwa a hakika akoi fa'ida sosai ga haka.


Kamarsu; lemu, cashew, abarba, kankana, Kara's, kwakwa da kuma shan ruwan ta, ayaba, inabi, tuffa, da dai sauransu.


Haka kuma za'a iya amfani da su coconot oil, cheese, peppers, zinc, strawberries, flax seeds, kidney beans, da kuma avocadoes.


Mataki na 4 ka nemi wadannan magungunnan da ake kira da natural medicines wadanda basu da wani lahani a jiki dukansu daga tsirran itatuwa ake yinsu.


Pine pollen and maca root powder.

  

Tribulus trestiries.


Libido booster 


 Horny goat weed.


L-Arginine


Za ka iya amfani da biyu ko uku a lokaci guda amma kada ka nemi wadanda ba su ba. ka tabbatar sune ka siya dan idan baka san products din ba to za'a iya baka wadanda ba su ba wanda wani lahanine daban kuma ba za su amfanar dakai ba.


Mataki na karshe sai a rikka motsa jiki akai-akai, dan kada a ci a koshi a koma waje guda a jibge.


A daina shan kayan zaki (sugary foods) da kayan maiko.


A rika samun isashen bacci.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post