Hausa-Fulani kalma ce da ake siffanta wata al'umma a arewacin Najeriya, wacce kuma ta daɗe tana jawo muhawara a kafofin sadarwa na zamani, wato social media.
Tambayar da ake muhawara a kai dai ita ce, "Shin ku Fulani ne ko Hausawa ko Hausa-Fulani?"
Wasu masana dai sun yi tsokaci a kan cewa babu wata ƙabila mai suna Hausa-Fulani, ko da yake sun amince cewa mutum na da damar ya siffanta kansa yadda ya so.
Farooq Kperogi mataimakin Farfesa ne a Jami'ar Kennesaw da ke Atlantar Jihar Georgia ta Amurka, kuma mai bincike a kan asalin ƙabilu, a wata hira da ya yi da BBC ya ce har yanzu ba a iya samun taƙamaiman asalin kalmar Hausa-Fulani ba.
Ya ce, "Abin da na sani shi ne jaridun Lagos da Ibadun ne suka sa kalmar ta shahara."
Tun a shekarar 1920 aka fara ambatar kalmar Hausa-Fulani. Kuma a cewar Farfesa Kperogi, dalibai irin su Ahmadu Bello sun yi amfani da ita a kwalejin Barewa sakamakon samun mutanen da a ƙabilance Fulani ne amma da Hausa suke magana.
Kansancewar an rasa yadda za a siffanta su sai aka kira su da Hausa-Fulani. Farfesa Kperogi ya ƙara da cewa, "ina ganin 'yan siyasar Kudu maso yammacin Najeriya ne dalillin shaharar kalmar."
Ya cigaba da cewa hakan ya faru ne saboda wahalar tantance asalin arewa saboda addini ya yi tasiri a wanan ɓangaren.
A kwana a tashi kalmar Hausa ta zama wata kalmar da ba ƙabila take alamtawa ba.
Kamar yadda Dakta ya bayar da misalin cewa za a iya samun Bayarbe ko Ibo wanda ya koma arewacin Najeriya da zama ya hayayyafa. Idan 'ya'yansa suka rungumi Musulunci suka kuma iya harshen Hausa sosai, shi ke nan sun zama Hausawa.
Fulani da yawa sun zama Hausawa a harshe, kamar wasu mutanen da dama.
Farfesa Kperogi ya yi bayanin cewa a yunƙurin siffanta kaka-gidan da 'yan arewa suka yi a fagen siyasa, da farko an zaci cewa ba Hausawa ba ne, saboda a kan basu suna Hausa Fulani.
Ya ce, "Amma kalmar ba tana nufin dunƙulewar Hausawa da Fulani ba ne".
A haƙiƙanin gaskiya abin da ake nufi a yanzu shi ne Musulmi ɗan arewacin Najeriya mai amfani da harshen Hausa.
Sai dai kuma wasu masanan sun ce akwai Hausawa da Fulani waɗanda ba Musulmai ba ne.
Farfesa Kperogi ya tabbatar da hakan, sai dai a cewarsa basu da yawa. Kuma saboda yawansu bai taka kara ya karya ba, mutane ba sa lura da hakan.
Kasancewar ƙAbilar Hausa ta ɗamfara da Musulunci kuma hakan ne ma yasa a cikin al'ummar Hausawa, waɗanda ba Musulmi ba sai ake kiransu Maguzawa.
Duk faɗin Afrika babu wani misali na mutanen da suka cuɗanya ta fuskar harshe da al'adu kamar Hausawa da Fulani.
A Rwanda 'yan ƙabilar Hutu da Tutsi sun gauraya ta hanyar auratayya, amma yawan hakan bai taka kara ya karya ba, shi yasa babu wani abu kamar Hutu-Tutsi, saboda ko wannensu bai bar asalinsa ba.
Amma a ƙalla a Najeriya duk inda Fulani suka je, ban da kudu maso gabas, su kan ajiye Fulatancinsu su ɗauki al'adu da harsunan mutanen da suka samu.
Kuma kasancewar Hausa ƙabila ce da ta fi yawan mutane a Najeriya da ma Afirka ta yamma, Fulanin da suka shiga cikinsu sun sarayar da harsunansu da al'adunsu.
A Afirka, al'ummar Fulani su ne suka fi kowacce ƙabila yaɗuwa a yammacin nahiyar, ana samunsu a ko ina, amma basu da rinjaye sai a Guinea. Kuma a ƙasar Hausa ne kawai suka yi cakuɗuwa ta ƙut-da-ƙut har suka sarayar da harshensu da ma ƙabilarsu.