Abubuwa 8 da ke sa siraran mata tsiwa da Iya Yi - Android Pols
An yi wani bincike mai zurfi da kuma tattaunawa da mata domin sanin dalilan da ya sa siraran mata suka fi sauran mata tsiwa, taƙwarƙwasa da kaɗifiri.


An tattaro wasu dalilai da suka sa hakan ya yi wa mata sirara rawani a koda yaushe.


1. Siraran mata sun fi sauran mata tsiwa da yaƙalƙalewa saboda, rashin girman jiki da suke da shi. Jikin na su fayau yake saboda haka rashin kunya salamu alaikum.


2. Suna ganin maza sun fi son siraran mata. Kafin ka ga namiji da ke son mace ɓakutu, sai ka ci karo da waɗanda ke son mata sirara 20. Wannan kuma wani tsari ne kawai da wasu mazan ke so.


3. Kazar-Kazar, Saboda kazar-kazar da suke da shi, suna ganin baka isa a kan su ba.


4. A ganin su sun fi kyau. Siririyan mace tun ba fara ba, gani take babu wanda ya fi ta kyau. Tsiya da yanga, babu kama kafan yaro.


5. Siririyan mace ta na ganin idan ta cika sassauci za a raina ta. Saboda haka ba za ta ɗaga ma kowa kafa ba. Idan kace mata cas, zata ce maka kule.


6. Daɗi da Saukin sha’ani a lokacin saduwa, Wasu da dama cikin maza sun ce, siririyar mace mara jiki ta fi juriya a lokacin saduwa. Sannan kuma zaka iya murginata yadda kake so ba kamar ɓakutu ba.


7. Ado ya fi musu kyau fiye da lutiya, Da yawa cikin mata da maza da muka tattauna da su, sun ce idan siririyar mace ta rangaɗa maka ado, ta fi jan hankali fiye da na mai jiki.


8. Ko kayan sa wa, idan mace siririya ta saka kaya za ka ga ya fi zama daram a jikin ta, komai ya bi jiki. Ba kamar lutiya ba.


Duk waɗannan sune ke rudar da zuga siriran mata su rika zubar da rashin kunya yadda suke so ba tare da sun damu da yadda mutane ke ji ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post