Dalilan Dake Haddasa Jinkirin Aure Ga Samari Da Ƴan Mata A Wannan Zamanin - Android Pols
Barknmu da kasancewa daku a wannan fili da fatan muna cikin ƙoshin lafiya. A yau za ku ji wasu dalilai guda 8 dake haddasa ko jawo a samu jinkirin yin aure, kodai ga budurwa ko kuma ga saurayi. 


Lokuta da dama zaka samu wasu ƴan matan sunyi shekaru na isa aure har sun ƙetara ba tare da sun yi aure ba haka suma mazan, kuma yawanci zaka samu lafiyar su ƙalau ba wani abu ne ke damun su ba. Shiyasa muka gudanar da wasu bincike muka kawo muku kaɗan daga cikin dalilan dake jawo hakan.


(1) Ra'ayi;

Ra'ayi yana daga cikin abinda ke haddasa Jinkirta Aure musamman ga ƴan mata. Akwai matan da suke da wani ra'ayi cewa su ba za su yi aure ba sai sun kai wani geji. ma'ana ita ba za ta yi aure ba sai ta samu mai Kuɗi, Ko kuma sai ta gama kartu ta samu aiki, ko sai ta samu jari mai ƙarfi, ko kuma tace sai ta samu namiji irin kalar da ya dace da ita da sauran su.


Shima saurayi anasa ɓangaren yakan sa aransa cewa sai ya samu ƴar gidan masu kuɗi sannan zai yi aure. ko kuma sai ya tara kuɗi masu yawa sannan zai nemi mace yai aure. To duk wannan ra'ayi ne da wasu daga cikin samari da ƴan mata keda shi wanda ke jawo musu jinkirin yin aure


(2) Talauci;

Talauci abune dake kawo cikas wajen yin aure da wuri musamman ga samari. Mafi yawan samari sukan kasa yin aure da wuri ne a dalilin rashin abin hannu. Wasu samarin zaka samu ko aikin yi ba su da shi, baya iya biyan buƙatar kansa balle kuma ta wani. Da yawan samari suna matuƙar son suyi aure, amma mahaifan su ba su da halin da za su iya aurar da su saboda halin talauci.


(3) Matsalar Aljanu ;

Wata babbar matsala kuma dake addaba samari musamman ƴan mata shine matsalar shafar Aljanu. Yana daga Sharrin Aljanu mazansu ko matansu, idan suna son mutum sukan iya shiga jikin sa su hana shi yin aure, ko da sun barshi yana soyayya amma da zarar Amfara maganar aure sai maganar ta lalace, wanda idan iyaye ba su yi dagaske ba shikenan yarinyar ba za ta yi aure ba haka za ta yi ta zama.


(4) Salon Yaudara;

Wani Ko wata, idan suka aminta da wanda suke so, daga bisani kuma sai yaudara ta shiga tsakani, daga nan fa sai su tsani junansu har soyayya da maganar auren su ta wargaje. Hakan ke jawo su koma karatu ko kuma wata harkar, har sai sun daina jin zafin raiɗaɗin cin amanarsu da aka yi sannan sai su fara tunanin yin aure.


(5) Rashin Lafiya;

Wannan ya shafi ɓangaren sha'awa, da Rashin lafiyariyar jiki, domin zaka ga wasu samarin ko ƴan matan suna da halin yin auren amma kuma sam basa ma son ai musu maganar auren saboda su basu san mene auren ba domin basa jin wani abu da ya danganci sha'awa.


(6) Al'ada;

Biyewa al'ada na matuƙar kawo naƙasu wajen gudanar da aure akan lokaci. Sai kaji sai an gudanar da wasu abubuwa masu yawa kafin ayi aure, misali sai ace sai anyi akwati seti 8, 10 ko sama da haka, sannan shima sadaki sai ace sai an biya adadin Naira Kaza, da sauransu. Shima yin wannan tsarabe-tsaraben yana taka muhimmiyar rawa wajen tsaikon aure.


(7) Sabon Allah (SWT);

Yana daga cikin abinda ke haddasa jinkirin aure fiye da tunani, har yakan haramta wa mutum samun damar yin auren ma. domin shi aure rahama ne, Rahamar Allah Kuma ba'a samunta ta hanyar saɓa masa.


(8) ƙaddara;

Wasu samarin zaka same su da halin yin auren, komai Allah ya hore musu. Sai dai kuma ba auren ne basa so ba, kawai Allah ne bai ƙaddara musu za su yi da wuri ba. Wasu duk yadda suka kai ga son yin aure, Idan lokacin da Allah ya ƙaddara musu baiyi ba, sai kaga sun daɗe ba su yi auren ba.


Wannan sune kaɗan daga cikin wasu dalilai dake jawo ko haddasa jinkirin aure ga samari da ƴan mata a wannan zamanin namu da muke ciki. Ina fatan duk wanda yake da wata lalura ko wata matsala daga cikin abubuwan da na ambata, ya Allah ka taimake shi wajen ganin an warware matsalar.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post