Hanyoyin Warware Matsalolin Ma’aurata - Android Pols



Ku himmantu ga ƙaunar juna gaya, domin ƙauna takan yafe laifuka masu ɗumbun yawa. Bayan aurenku, matsaloli dabam-dabam za su kunno kai.


Waɗannan matsalolin suna iya tasowa a sakamakon bambancin ra’ayi da bambancin tunani da kuma yadda kuke tafiyar da rayuwa. 


Ƙari ga haka, matsaloli suna iya zuwa daga wurare dabam-dabam har da abubuwa na ba-zato.


Maimakon mu guje wa matsalolin da muke fuskanta, ya kamata ku san hanyoyin da za mu magance su. Idan kuka bi ka’idodin hakan zai taimaka muku ku magance matsalolin ku. Ga jerin hanyoyin kamar haka ;


1 Ku Tattauna Matsalar:

“Akwai lokacin magana. ”Ku tabbata cewa kun tattauna matsalar sosai. Ka gaya wa matarka ainihin abin da ke zuciyarka da kuma ra’ayinka a kan batun. A kowane lokaci, ku gaya ‘wa junanku gaskiya.’ Ko da abin ɓacin rai ya faru, kada ku yi faɗa. Idan ka yi maganar da za ta sanyaya zuciyar matarka, ba za ku yi babban gardama ba.


Ko da ba ku jitu a kan wani batu ba, ku ci gaba da yi wa juna alheri. Kada ku manta cewa ya kamata ku riƙa nuna wa juna ƙauna da ban girma. Ku yi ƙoƙari ku sasanta matsalar da ke tsakaninku nan da nan, kuma kada ku ƙi yin magana da juna. Ku keɓe lokaci don tattauna matsalar da ke tsakaninku


Idan matarka tana magana, ka yi ƙoƙari ka ƙyale ta ta gama magana. Idan ta gama, sai ka yi magana.


2 Ku Saurara Kuma Ku Fahimci Juna: “Ku ƙaunaci juna gaya. Wajen ba da girma, kowa ya girmama ɗan’uwansa.” Yana da muhimmanci ka kasa kunne da kyau sa’ad da matarka take magana. Ka yi ƙoƙari ka fahimci ra’ayinta kuma ka yi hakan da ‘juyayi’ da kuma ‘tawali’u.


Kada ka yi kamar kana saurara kawai. Idan da hali, ka bar abin da kake yi gabaki ɗaya don ka saurari matarka sosai, ko kuma ka tambaye ta ko za ku iya tattauna batun a wani lokaci. Idan kuka ɗauki juna a matsayin abokai maimakon abokan gaba, ba za ku yi garajen yin fushi da juna ba.


Shawara : Ko da abin da matarka take faɗa yana ci maka rai, ka ci gaba da saurarawa don ka fahimce ta Ka mai da hankali ga abin da take nufi maimakon kalmomin da take furtawa. Ka lura da muryarta da kuma fuskarta yayin da take magana.


3 Ku Yi Duk Abin Da Kuka Shawarta:

 “A cikin dukan aiki akwai riba: Amma taɗin baki ba ya nufa koina sai wajen tsiya.” Yanke shawara mai kyau kawai ba shi ne aikin ba. Kuna bukatar ku yi abin da kuka shawarta za ku yi. Yin hakan ba zai kasance da sauƙi ba, amma za ku sami sakamako mai kyau. Idan kuka ba juna haɗin kai, za ku girbi ‘amfanin wahalarku.


Shawara: Kowannenku ya ƙudura yin abin da zai iya yi don ku warware matsalar da ke tsakaninku a lokaci-lokaci, ku zauna ku bincika don ku ga ko kuna samun ci gaba a wannan batun.


Ku Warware Matsalolin Ku Tare:

Idan kai da matarka kuka yi ƙoƙari sosai, aurenku zai yi daɗi maimakon ɗaci. Kada ku ta da maganar da ta riga ta mutu, amma ku mai da hankali ga gaba. Idan kuka ba wa juna haɗin kai kuma kuka bi ƙa’ida za ku iya warware duk wata matsala da ta kunno kai.


Ka Tambayi Kanka 


Wace matsala ce nake bukatar tattaunawa da matata cikin gaggawa?


Me zai taimaka mini in fahimci ra’ayin matata a kan wannan batun?


Wadannan hanyoyin za su taimaka muku wajen kawo karshen matsalolin da ma'aurata suke fuskanta a zamantakewar aure. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post