Saurin Inzali(Kawowa) A Yayin Jima'i Da Yadda Za Ku Yi Magani - Android Pols


Biyan bukatar namiji da mace wajen jima'i yasha banban ta fuskar tsawon lokaci. Kashi 68 cikin 100 na mata suna bukatar minti 8 su biya bukatarsu da mazajensu, haka kuma, kashi 45 na wasu matan na bukatar minti 12 yayin saduwa. 


Abin mamaki shine, kashi 75 na maza na kasa jurewa su tsawaita lokacin biyan bukatarsu zuwa minti 3 ko 6, sabanin lokacin da wasu matan ke bukata don biyan bukatarsu. (Qinghai Province Xining City Ailida Biotechnology Company, 2012).


Saurin inzali ko kawowa (القذف المبك/Premature Ejaculation) yanayi ne da namiji yake saurin biyan bukatar  jima'i da zaran zakari ya shiga farji cikin 'yan daƙiƙoƙi ko mintuna kaɗan koma kafin shigar zakari cikin farji kasancewar namijin baya iya tsawaita lokaci ko jure dadin jima'in da yake ji na tsawon wani lokaci, musamman saboda matsannanciyar sha'awa ko kamuwa da yawa. Saurin inzali na faruwa ba tare da mutum yayi niyyar yin hakan ba. Jima'i a wannan yanayi na  karewa da zaran maniyyi ya fita daga jikin namiji. A wannan yanayi namijin ba ya iya yiwa sha'awarsa linzami ta fuskar rage sauri domin more jima'i na tsawon wani lokaci kuma baya iya gamsar da iyalinsa wacce saurin inzali ke hanata biyan bukatarta, ko haddasa rashin gamsuwarta. Kasancewar mata na bukatar lokaci mai tsayi fiye da na maza mafi yawan lokutta.


Shekaru da dabaru na yau da kullum saboda fahimtar jima'i tsawon lokaci a rayuwa nasa maza su fahimci yanda za su magance matsalarsu da kansu ba tare da wani magani ba wani lokacin.


Abubuwan Da Ke Haddasa Saurin Inzali / Kawowa 


Haryanzu dai babu wani sahihin bayani ko dalili dake bayyana dalilin saurin kawowa ba, sai dai wasu bayanai akan dalilan da ka iya bada haske game da matsalar saurin kawowa ga maza (premature ejaculation). Sune kamar haka:


1. Matsalar rashin karfin mazakuta  (erectile dysfunction). Idan namiji baya da karfin gaba to akwai yiwuwar asami saurin kawowa lokacin jima'i, haka kuma, idan akwai karfin zakari to akwai yiwuwar dadewar yin jima'i mai tsawo tsakaninin ma'aurata biyu. Saboda haka, saurin inzali na iya zama wani lokacin alama ce ta rashin karfin zakari.


2. Yanayin halittar wasu mazajen. Wani haka Allah Ya halicce shi ko minti 1 baya iya yi da mace. Amma wannan baya nufin baza'a iya samun saukin yanayin ba. Za'a iya neman magani ko Allah Yasa a dace.


3. Samuwar hadari (accident) wanda zai iya shafar al'aurar mutum. Hadari wanda ya shafi lafiyar al'aura  na iya haddasa matsalar saurin kawowa.


4. Magungunan kayan mata/da'a da  mata ke yi. Magunguna na matsi da mata ke sakawa cikin gaba domin matse/tsuke farji. Idan mace tayi amfani da wani magani gabanta ya tsuke/matse fiye da yanda maigidanta ya saba jinta zai iya sa maigidan yayi saurin kawowa saboda karuwar dadi ko dandanon jima'i.


5. Cututtuka masu shafar lafiyar jima'i, kamar cututtukan sanyin mara na maza da mata.


6. Ciwon damuwa ko fargaba na iya  haddasa saurin inzali. Misali, idan mutum yayi sabuwar amarya budurwa ko bazawara , idan yana fargabar ko zai iya gamsar da ita ko damuwa akan wani abu, wannan tunani zai iya sanya saurin inzali a cikin saduwar su.


7. Yin istimina'i da gaggawa ( quick masturbation) da wasu matasa keyi kamin  suyi aure, musamman yara don gudun kada a kamasu (wasa da al'aura ko zinar hannu). Yana shafar lafiyarsu, yana haddasa saurin kawowa lokacin jima'i.


8. Gado daga wajen mahaifan mutum (inherited traits). Akwai yiwuwar mutum yayi gadon saurin kawowa daga mahaifinsa ko kakansa ko wani jininsa, wato tsatstsonsa. Wato haka duk "family" nasu suke amma bai sani ba.


9.  Matsananciyar sha'awar yin jima'i. Idan mutum ya kosa  yayi jima'i, fitinar sha'awarsa ko kamuwa da yawa za ta iya sanya shi yayi saurin kawowa da zaran zakarinsa ya shiga jikin mace ba tare da bata wani lokaci ba.


10. Rashin wasanni tsakanin ma'aurata kafin saduwa ta yanda macen zata iya fara biyan bukatar ta da wuri kafin maigida ya fara jima'i da ita ta gaba da gaba .


11. Sauyin abokiyar saduwa/ sabuwar amarya budurwa ko zawara. Yanayin sabuwar abokiyar rayuwa, wato sabuwar amarya ga maigida na da tasiri ga kwalwar namiji, yana sanya namiji ya rikice ko ɗimauce da ɗauki wanda hakan zai sanya shi saurin kawowa. Bugu da kari, Binciken ilimi na kiyimiyya ya nuna cewa samun sabuwar abokiyar saduwa (mata)  na sanya maniyyin namiji inganci da kyau fiye da nada.


14. Canza salon kwanciyar aure, musamman mutum kada yayi kwanciya da iyalinsa wacce zata sa zakarinsa ya shige duka cikin gaban ta. Nutso (deep penetration) nasa saurin inzali.


13. Nau'in wasu magungunan. Akwai wasu magungunan da "side effects" nasu zai iya haddasa saurin kawowa ga mutum. Da sauransu, mu takaita haka.


Magance Matsalar Saurin Kawowa 


Hanyoyin magance saurin inzali suna da yawa, wasu hanyoyin na yiwa wasu aiki, wasu kuma sabanin haka, don haka ga hanyoyi kamar haka da mutum zai iya jarrabawa domin neman dacewa:


   a) Rage ƙosawa/ƙagara. Mai saurin inzali ya kamata ya cire tunanin jima'i daga ƙwalwarsa a lokacin da yake saduwa da iyalinsa. Matsanancin tunani ko kamuwa da yawa kafin fara jima'i zai iya sanya mutum "ya ƙone tun kafin ya tafasa".


Masana sun nuna cewa bujiro tunanin wani abu a cikin rai wanda ba jima'i ba marar daɗi a lokacin saduwa na ƙarawa mutum tsawon lokaci ba tare da ya lura da hakan ba. Ɗaukin jima'i baya biya, abinda zai taimakawa mai matsalar saurin kawowa shine, rage yawan tunanin jima'i ne yake aikatawa, ko kuma ya bar yin tunanin cewa yana yin jima'i ne domin samun gamsuwa wacce iyalinsa da yake sha'awa take biya masa.


 Kamata yayi tunaninsa ya kasance cewa yana aikata jima'i ne domin ya biyawa iyalinsa bukata farko kamin tasa. Abin lura, ka ɗauka ma cewa ba jima'i bane kake yi a lokacin da kake tarawa da iyalinka.


    b) A nemi kuɓewa ɗanya (okra) guda 5, a wanke sa'annan a yanke gutsun-gutsun a cikin tukunya, sai a sami kofi ɗaya na ruwa a zuba cikin tukunyar sa'annan a ɗaura akan wuta a rufe tukunya. Da zaran ruwan ya tafasa sai a sauke tukunya a tache ruwan a kofin shayi, sai a zuba zuma ta bada ɗanɗano, a bari ya huce kaɗan amma asha da ɗumi. Ayi haka sau 2 a rana har na tsawon kwana 10 ko fiye da haka. Kubewa na da sinadari mai amfani mai sanya jinkirin kawowa ga maza.


   c) A nemi citta (ginger) musamman ɗanya, a wanke a kuma  karkare ta, sa'annan a dake ta, ayi shayi da ita, bayan an tashe ta a kofin shayi sai a zuba zuma ta bada ɗanɗano asha shayin da ɗumi. Ayi hakan safe da rana. Citta na da sinadari mai zafi na  "gingerol" mai sanya yawan gudanar jini ga laura , wanda hakan na sanya ƙarfin gaba da jinkirin kawowa.


   d) A nemi man na'a-na'a (peppermint oil) mai kyau, musammman ɗan Misra ko na kamfanin Hemani (Pakistan). A wanke gaba da ruwan dumi, a goge lemar sa'annan a shafa man ga zakari ya shiga fata, ga kai (glans) da tsawon sandar zakari (shaft) , amma banda kofar fitsari (urethra).


 Musamman a shafa idan zakari yana mike,  sai jira bayan minti 10 zuwa 15 sa'annan a sadu da iyali. Man na'a-na'a na rage "sensitivity" na zakari, wato rage kaifin ɗanɗano da zakari keji ta yanda zai hana saurin kawowa lokacin jima'i. Haka kuma za'a iya amfani da man kanimfari (clove oil) mai kyau a maimakon man na'a-na'a. Bugu da kari, man kanimfari na maganin karfin gaba.


    e) Fita daga gaban mace na 'yan mintoci a lokacin da mutum yaji ya kusa kawowa, da kuma fita daga cikin farji da matse kan zakari da hannu (squeeze and pause technique/penis grip) a lokacin da mutum yake akan hanyar kawowa.


   f) Bayan kawowar farko, kawowa ta biyu na zuwa da lokaci mai tsawo kafin mutum ya sake fitar da wani maniyyin a karo na biyu. Don haka idan mutum yana son ya daɗe bai yi inzali ba to ya tari jima'i a karo na biyu wanda zai bashi lokaci mai tsawo kafin yayi inzali.


    g) Hanyoyin neman magani na musamman daga Likitan asibiti ko Malamin Islamic Chemist. Idan hanyoyin da muka zayyana basu yiwa mutum ba to sai yabi hanyar ganin ɗaya daga cikin wadannan mutanen domin neman taimako. Akwai wasu hanyoyi da dama na magance matsalar saurin inzali.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post