Ma'aikatar Shari'a a jihar Bauchi ta shirya taron Mukabala kan Sheikh Idris Dutsen Tanshi - Android Pols



Gwamnatin jihar Bauchi a karkashin ma'aikatar shari'a, ta gayyaci Sheik Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi, zuwa taron tattaunawa (Mukabala) domin  kare kansa bisa zargin furta kalamai na rashin ladabi akan manzon Allah, Annabi Muhammadu (SAW), cikin wani karatu da ya gabatar a wannan wata na Ramadan, inda yake cewa "Kai! na manzon Allahn ma bamu son taimakonsa karewarta kenan." 


Ma'aikatar Shari'a ta jihar Bauchi tace wannan kalamai zasu iya haifar da tunzuri kuma barazana ne ga zaman lafiya musamman ga wadanda suka yi Imani da addinin musulunci.


A saboda haka ne aka shiya wannan taro wanda za'a gabatar a ranar Asabar 8 ga watan Afrilu 2023, domin warware zare da abawa, kasancewar mutane da dama musamman malamai sun fara tofa albarkacin bakinsu, wadansu na ganin yayi kuskure, yayin da wadansu ke ganin bai aikata kuskure ba.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post