Ko Ka San Tsawon Lokacin Da Yakamata Ka Dauka Kana Jima'i Da Matarka?




Wani abu da yawanmu maza bamu gane ba shi ne yawan lokacin da ya kamata kayi akan matarka a yayin gudanar da jim'i da ita.


Duk da yake babu wani bincike da ya tabbatar da hakikanin tsawon lokacin da magidanci zai tsawaita akan matarsa ma'ana yana jima'i da ita, sai dai kuma binciken ya tabbatar da cewa mafi karancin lokacin da namiji zaiyi yana jima'i shi ne daga mintuna  3 zuwa 7, duk namijin da ya kasa daukar wannan lokacin yana saduwa da matarsa to tabbas yanada matsalar da ya kamata yaga likita.


Haka zalika mintuna 7 zuwa 13 sune yawan tsawon da idan namiji yayi a lokacin saduwa bai takurawa matarsaba shi ma bai jigata kansa ba, kamar yadda bincike ya nuna. Kamar yadda nazarin ya kara tabbatar da cewa mintuna 10 zuwa 30 akan mace ana jima'i da ita lokuta ne da suka wuce hankali ga maza masu irin wannan jimawan akan matansu. Sai dai wadannan tsawon lokutan basu hada da lokutan wasannin motsa sha'awa ba, ana lissafin lokutan ne daga lokacin da shi maigida ya shigar da azzakarin sa a farji.


Babban abunda ya kamata maza magidanta su kuma fahimta anan shine, ba wai ana nufin cewa dole ne sai maza sun dauki tsawon wadannan lokutan akan matansu ba, ko kuma su takaita kamar yadda kamar binciken ya nuna ba, abun da ya kamata maza su fahimta shine ana bukatar kowani magidanci ya iya fahimtar tsawon lokacin da matarsa take iya samun gamsuwa a jima'ince.


Akwai wasu matan a cikin mintuna biyu kacal sun biya bukata, akwai matan da a lokutan wasannin motsa sha'awa ma sun kawo, kamar yadda ake samun wasu matan muddin ba an dauki sama da sa'a guda ko rabin sa'a ana gurzarsu ba ba su san ma ana yi ba.


 

Masana sun bada shawaran cewa, ko wani magidanci dole ne ya fahimci matarsa sosai a jima'ince ta haka ne kawai zai iya gamsar da ita na babu cuta babu cutarwa. Ganin shi gamsar da mace a yayin jima'i dole ne akan dukkannin wani magidanci. 


Ga mazan da suke yin shaye shaye kafin su yi jima'i suna iya fuskantar Matsalolin ko dai a kamin tsufan su ko bayan tsufan su.


Ita mace ba wai tsawon lokacin da aka dauka akanta shine ke sata gamsuwa ba. Kawai magidanci yayi kokarin gano abubuwan da suke sauƙin gamsar da matarsa. 


Wasa da ita ne ko kuma saduwa da ita ke sata gamsuwa da wuri. A saduwa da ita dinma a wani yanayin kwanciyar jima'i take samun gamsuwa. Waɗanan sune abubuwan da maigida zai gano amma bawai sai ya yi shaye-shaye ba domin gamsar da matarsa.


Sai dai babu laifi lokaci zuwa lokaci namiji ya sha maganin da zai kara masa lafiya gaba ko karin Kuzari, amma kada kuma ya zame masa idan bai sha wani abun da ya saba sha ba ba zai iya gamsar da matarsa ba.


Wannan sune abubuwan da ya kamata maigidanta su gane domin taimaka musu samun zama cikin lafiya da matansu. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post