Yadda Tsamiya Ta Ke Yin Maganin Wasu Matsalolin Maza Da Mata - Android PolsKo kunsan cewa tsamiya tana da matukar amfani ga mata kai har da maza wajen inganta lafiyar al'aura, karin ni'ima ga mata da kuma bayar da kariya daga kamuwa da wasu cuttuka.


Ana samun tsamiya a kasashen Africa da sauran wasu sassan duniya. Tsamiya na rage kitse sannan tana inganta lafiyar zuciya sannan tana taimakwa wajen magance cutar mura, masassara, matsalolin mafitsara, hanta, rikichewar ciki, matsalolin daukar ciki ga mata da kuma kara lafiyar sassan al'aurar mata da na maza baki daya.


Ga jerin amfanin da tsamiya ke yi ga mata kamar haka:


(1) Tsamiya na kara lafiya ga sassan haihuwa  ga mata da kuma taimakawa wajen inganta cikakkiyar lafiya wajen daukar ciki a cikin sauki. Saboda haka duk Macen da ke da matsalar haihuwa za ta rika yin shayin tsamiya safe da yamma insha Allah za ta samu biyan bukata domin tsamiya na dauke da sanadarin vitamin C da yake taimakawa wajen magance matsalolin da ka iya hana daukar ciki.


(2) Kari ni'ima, duk Macen da ke fama da karanci ko daukewar ni'ima idan ta tsaya akan shayin tsamiya kadai zai bata cikakkiyar ni'ima domin dawo da kimar ta wajen maigida domin rashin ni'ima ga mace tamkar abinci ne ba maggi.


(3) KARA GIRMAN NONO: Tsamiya na taimakwa wajen samun girman nono, bama tsamiya kadaiba duk wani kayan marmari mai dan tsami kamarsu lemon zaki, mangoro da dai sauransu suna kara girman ga mata. Shan shayin tsamiya akalla sau biyu a rana babu shakka yana kara girman nono. 


Yadda za'ayi shine za'a samu tsamiya hudu ko biyar a jika da ruwan dumi a dame ruwan a shanye na tsawon sati daya bayan ansha sai ajira kada asha ruwa sai bayan awa daya   indai ana haka insha Allah za'a sha mamaki.


(4) YAKI DA CUTTUKAN DA AKE DAUKA WAJEN SADUWA: Tsamiya na dauke da sinadarin vitamin C wanda yakan bada kariya wajen daukar wasu cuttukan waje saduwa sannan shi vitamin C din yakan inganta lafiyar maniyyi.


(5)  maganin masassara


(6) Tsamiya na taimakama masu ciwon sugar.


(7) Tana bada kariya daga kamuwa da ciwon zuciya.


Da fatan za'a amfana daga cikin wadannan jerin amfanin da tsamiya ke yi a jikin dan adam musamman mata. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post