Amfanin Yayan Kabewa Ga Mata Da Maza - Android Pols


'Yayan kabewa wasu yayane masu kama da yayan kankana sai dai sunfi yayan kankana girma. Ana samunsune a tsakiyar kabewa bayan anfasata.


Sanadiyyar rashin sanin amfanin wannan yaya mutane dayawa sukan zubda wadannan diya bayan suna da alfanu sosai ga rayuwarmu ta yau da kullum.


Yayan kabewa suna dauke da sunadarin antioxidants wadanda ke bayarda kariya daga kamuwa da wasu cututtuka ga dan adam.


Bayan haka ana sarrafa wannan yaya na kabewa domin inganta lafiyar maniyyi saboda yayan kabewa na dauke da sinadarin zinc , sinadarin zinc yana inganta lafiyar alaura sannan yana kara sha'awa da kuma karin ruwan maniyyi lafiyayye ga maza da mata


INGANTA LAFIYAR JARIRI A CIKI.


Sinadarin zinc dake kunshe da yayan kabewa na karfafa garkuwar jiki. Idan mace na dauke da juna biyu tana amfani da garin yayan kabewa to insha Allahu cikinta ba zai zube ba sannan jaririn zai samu cikakkiyar lafiya.


YADA AKE AMFANI DA YAYAN KABEWA.


(1) za'a samu cokali guda na zuma da rabin cokalin garin yayan kabewa asha da safe kafin a karya.


(2) ko a sha rabin cokalin acikin yoghurt.


(3) ana zubashi cokali daya a miya asha yana karawa jiki lafiya sosai.


Allah yabamu dacewa.

A turawa yan uwa su amfana


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post