Irin Halin Da Zawarawa Suke Tsintar Kansu Bayan Mutuwar Aurensu - Android Pols

 


Hakika zawarcin 'ya mace masifa ne, mutuwar aure ba dadi sai ya zama dole, kuma mace tafi fuskantar kalubale da barazana da matsaloli a dalilin mutuwar aure. 


Idan kana zantawa da bazawara tana baka labari abinda take fuskanta a zaman zawarci tun daga cikin gidansu da kuma mutanen da zasu sake zuwa neman aurenta sai ka tausaya wa duk wata bazawara. 


Kashi 99 cikin 100 na zawarawa da samarin da zasu je neman auren bazawara iskanci da lalata yake kai su, saboda suna ganin ai ta san komai game da sha'anin aure, zasu fi samun saukin yaudaranta akan budurwa, don haka sai wacce Allah ya tsallakar a cikin mata zawarawa. 


Ba daidai bane bazawara ta jima a gida bata sake yin wani auren ba musamman idan tana da manema, da zaran kunga ta fara rike wayoyi manya, tana sayan zannuwa masu tsada, ba aiki ko sana'a take ba, to ba shakka wannan ta fada ruwa. 


'Yan uwa ma'aurata a cigaba da hakuri da juna, rabuwar aure babu dadi sai idan ya zama dole, zawarci babu dadi Sam, Allah Ya rufa asiri, Ya hada kowa da rabona. 


Mata da yawa suna rayuwar aure cikin ƙunci saboda suna auren aljihu (kuɗi) maimakon kyawawan ɗabi'u.


Wasu mazaje suna ƙuntata a rayuwar aure saboda sun auri kyan sura da jiki, ba kyan halayya ba.


Mutane da yawa (kuma) a yau, suna shiryawa bikin aure ne (kaɗai) ba zaman aure ba, wannan ya sa muke ganin sake-saken aure ya yi araha, duk da ruwan soyayya da ake nunawa a gari da 'media'. 


Ya Allah! Mun bar maka zaɓin rayuwarmu a hannunka, ka iya mana ba da wayonmu ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post