Nine Halastaccen Shugaban Kasar Nigeria Domin Ni Na Ci Zabe kuma kotu za ta karbar min, Peter Obi




Ɗan takarar shugaban ƙasa na Najeriya a ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun hamayya, Labour Party, Peter Obi ya ce shi ne ya ci zaɓen da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu 2023.


A cewarsa zai bi duk wani matakin shari’a domin ya ƙwato nasarar da ya samu cikin karamin lokaci.


Mista Obi ya ce wannan ne karon farko da ya fito duniya yake magana tun bayan kada kuri’ar da ya yi a zaɓen, saboda haka ya ce duk wani sako ko magana da aka danganta da shi a baya ba shi ya fada ba.


"Mun ci zaɓen kuma za mu tabbatar wa da 'yan Najeriya hakan," in ji Obi.


Yaya kuke ganin wadannan kalaman na Peter Obi?


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post