Bayan Shafe Makonni A Gidan Yari Murja Ibrahim Da Mai Wushirya Sun Shaki iskar 'Yanci


Wata kotu a Kano ta sako Murja Ibrahim Kunya tare da Ashiru Idris Mai-Wushirya, bayan zaman gidan yari na sama da makonni biyu.


Sai dai kotun ta kafin ta sako su, ta ce Murja Kunya za ta yi sharar asibitin Murtala har tsawon makonni uku, sannan za ta dauki tsawon watanni shida tana ziyartar hukumar HISBAH.


Haka zalika kotun takuma ce, Mai-Wushirya, BBC, da kuma Sadik Shariff an umarce su da su yi sharar masallacin Murtala na tsawon makonni uku.


Rahotanni daga jihar Kanon na cewa, zauren malaman Kano ne ya gurfanar da matasan gaban kotu, bisa zarginsu da wallafa kalaman batsa a dandalin TikTok.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post