Babu Wanda Ya Bani Kyautar Gida Ko Mota Tun Bayan Ibtila'in Da Ya Same Ni, Cewar Rarara


Fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (RARARA) ya musanta jita-jitar da ake yi na cewa an bashi kyautar Motoci da Gidaje, bayan wani iftila'i da ya fada masa.


Tun a ranar 20 ga watan Maris ne dai mawakin siyasar aka samu wasu fusatattun matasa da suka ɓuge da murnar cin zaben Abba-Gida-Gida suka kai farmaki Rarara suka ƙone masa motoci tare da sace kayan gidan.


Wanda tun bayan hakan wasu labarai a kafafaen sada zumunta ke ta yawo cewa wasu ƴan siyasa sun yiwa mawakin kyautar motoci da gidaje.


Sai dai a yau ne Rarara ya fito ya ƙaryata wannan labaran da wasu mutane ke ta yayayatawa a kafafaen sada zumunta, indai yai kira gare su da su daina ƙirƙirar abinda ba haka bane.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post