Wata Sabuwar Amarya Ta Nemi Angonta Ya Saketa Kan Kin Bata Kudin Da Za Ta Yi Bikin Birthday


Wata sabuwar amarya ta watsawa Angonta ruwan sanyi a jiki saboda ya hanata kudin da ta bukata don murnar zagayowar ranar haihuwarta a jihar Kano.


Daga bisani ta bukaci ya sake ta, ba ta son auren. Amaryar mai suna, Fatima Bashir Alkali, ta gurfana gaban kotun Shari'a dake unguwar Post Office kan abinda ta yiwa mijinta, Alhaji Nura Gambo, rahoton DailyTrust. 


Fatima Bashir Alkali wacce aka fi sani da Yar Albarka ta gurfana gaban Alkali Nazifi Adam kan tuhume-tuhume 3 wanda suka hada da ta'adi kan hakkin mijin, yaudara, da ha'inci.


Lauyan mijin, Badamasi Gandi, ya bayyanawa kotu cewa Amaryar ta bukaci mijinta ya bata wasu kudade don murnar zagayowar ranar haihuwarta amma ya ki, sai ta musguna masa sannan ta bukaci saki.


Gandu ya bayyanawa kotu cewa idan tana son mijin ya sake ta, ta ba shi N10m kudin da ya kashe mata lokacin aurenta. Amma Yar Albarka ta musanta zargin da ake mata kuma an bada belinta saboda har yanzu akwai aure tsakaninsu kuma an dage zaman zuwa ranar 3 ga Maris.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post