Na yi shekaru Babu Aure Kuma Maza Basa Zuwa Neman Aurena Domin Suna Tsoron TunkarataFitacciyar jarumar Kaddara Etiko ta bayyana halin da take ciki na rashin samun mijin aure tsawon shekaru. 


 A cewarta, a shirye take ta fara soyayya da kowane irin namiji muddin zai bata kula kuma ya faranta mata, duk da cewa a zabin ta tafi son namiji wayayye.


Matsalar shine maza suna tsoron tunkaro ni su yi min maganar aure saboda suna tunanin cewa ko akwai wani da yake sona ko kuma ba zan karbi soyayyar su ba. 


“Haka zalika, har yanzu ina iya zama mara aure saboda yawancin mutane suna tunanin cewa mashahuran mutane ba da kowa suke iya yin soyayya amma wannan fahimta ce mara kyau.


Yawancin mashahuran mutane ba su da aure saboda sun ruɗe game da wanda za su karɓa a rayuwarsu. Ka ga, ba ka da tabbacin ko mutumin yana sonka ne saboda shahararka da kuɗinka ko kuma mutum yana son kasancewa tare da kai saboda soyayya ta gaskiya.


Ba na son mutum ya so ni don ina da kudi ni duk wanda yake so na ko zai so ni to son gaskiya nake so ba na kudi ba. 


Da ake tambayarta shin ko ta samu namijin da ta ke mafarkin samu? Tace aa, amma dai tana sa ran nan da dan lokaci kadan za ta samu. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post