Maishadda Ya Mayar Da Martani Ga Masu Caccakar Su Kan Ziyarar Da Suka Kai Gidan Halima Atete


Fitaccen furodusan nan Abubakar Bashir Maishadda ya yi martani kan ƙurar da ziyarar da shi da wasu ‘yan Kannywood su ka kai wa tsohuwar jaruma Halima Atete a gidan mijin ta a Maiduguri, Jihar Borno.


Maziyartan, waɗanda su ka dira a gidan a ranar Juma’a da ta gabata, sun haɗa da  Bashir Abubakar Maishadda, Yakubu Muhammad, Garzali Miko da Ibrahim Sharukan.


Shafin Mujallar Fim ta ruwaito cewa tun bayan bayyanar hotunan ziyarar jama’a da dama su ke tofa albarkacin bakin su, musamman a Kafar soshiyal midiya. Yayin da wasu ke ganin abin burgewa ne, wasu kuma na ganin sam ba su kyauta ba, wai wannan wani salo ne na hana ta zaman gidan miji ko kuma su sa hankalin ta ya dawo kan harkar fim har ta juya wa mijin ta baya.


Ganin yadda maganar ta ke ci gaba da yamutsa hazo ne ya sa mujallar Fim ta nemi jin ta bakin ɗaya daga cikin ‘yan fim ɗin da su ka kai ziyarar, wato Maishadda, don jin abin da zai ce game da surutan da ake yi.


Furodusan ya ce: “Rabu da mutane kawai a kan maganar da su ke faɗa! Mu dai da kyakkyawar manufa mu ka yi.”


Maishadda ya ƙara da cewa, “Ba wai takanas mun je gidan Halima Atete ba ne, a’a, wani uzirin mu ne ya kai mu garin, kuma sai mu ka je gidan ta a matsayin ta na ‘yar’uwar mu, mu ka ziyarce ta a gidan ta. Don haka mu abu ne mu ka yi da kyakkyawar manufa.


“Masu magana kuma su je su yi ta yi, mu dai ziyarar sada zumunci mu ka je yi ba don mu kashe mata aure ba.”

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post