Yadda Wata Mata Ta Kone Kanta Saboda Gaza Biyan Bashin Dubu 70 Da Ake Binta
Wata mata a Abekuta ta cinna wa kanta wuta ranar Asabar saboda bashin N70,000 da bankin kananan masana’antu ke bin ta.


Matar mai suna Mama Dada ta kona kanta da gidan da take haya ne a unguwar Oke-Keesi da ke Karamar Hukumar Abekuta.


Wani ganau mai suna Rasheed Aina ya bayyana wa shafin Aminiya cewa  gawar margayiyar ta kone kurmus kafin a ciro ta.


“Bashin wani fitaccen bankin masanaantu na yankin ta karba har na N70,000 ta kasa biya, shi ne ta kona kanta”, in ji shi.


Ya kara da cewa,”Wani tsohon ma’aikacin bankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce tsarin bankin shi ne duk wanda ya gaza biyan bashin a wani kayyadajjen lokaci, tozarci zai biyo baya.


“Ba karamin tozarci nake nufi ba, irin wanda har ’ya’yanka sai sun kasa shiga mutane ne.”


Rahotanni dai na nuna cewa an kai gawar margayiyar dakin adana gawa da ke Babban Asibitin Ijaye a jihar.


Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce basu samu labarin lamarin ba, amma za su gudanar da bincike.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post