Sun yi aure bayan haduwarsu a Soshiyal midiya cikin watanni 7


Duk da tsegumi da ake yi akan illolin da yin amfani da shafukan soshiyal midiya ke da shi cewa yana lalata tarbiyyar mutane tare da kashe aure da jawo yaɗuwar zinace-zinace.


Sai dai idan aka kalli tasirin kafafen sada zumunta suna taka muhimmiyar rawa wajen hada zumunta, aure da cinikayya tsakanin al'umma a sassa daban-daban na duniya.


Wani labari da ya dauki hankalin al'umma shine na auren wasu matasa da suka hadu a shafin sada zumunta na twitter wanda har ya kai ga sun yi aure.


A Hotunan auren su da ta wallafa a ranar Alhamis 22 ga watan Disamba amarya Fatima ta bayyana yadda ta hadu da angonta Umar Yahaya watanni 7 da suka gabata a shafin Twitter.


Fatima ta ce hirar su da angonta ta fara kamar wasa, kawai ya yi mata sakon Barka da Sallah ne daga haka kuma sai hira ta shiga tsakaninsu har Allah ya hada jininsu suka fara Soyayya.


A rubutun da ta wallafa a shafinta na twitter Fatima ta ce:


”A karshen makon nan wani abu ya gudana wanda na manta ban sanar muku ba…. Na auri wanda nake so watanni bakwai bayan mun haɗu a Twitter. Na godewa Allah.”


A nasa rubutun, ango Yahaya yace:


“Alhamdullilah, Allah ya albarkaci rayuwar auren. Bazan kuma iya bayyana irin son da nake miki ba.”

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post