Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100 a yayin wani farmaki



A wani sumame da rundunar sojin Najeriya ta  Operation Hadin ta kai a arewa maso gabas a maboyar yan bindiga na ISWAP da Boko Haram ta hallaka guda 103, rahoton RFI Hausa.


Daraktan sashen yada labarai na Ma’aikatar tsaron Najeriyar Musa Danmadami da ke bayyana hakan jiya alhamis a Abuja ya ce dakarun sun kuma yi nasarar kame ‘yan ta’adda 22 ciki har da kwamandoji 4 baya ga wasu mutane 18 da ke taimakawa ‘yan ta’adda.


Janar Musa Danmadami ya kuma bayyana yadda dakarun Sojin suka kubutar da fararen hula 30 da ke tsare a hannun ‘yan ta’addan yayin Iyalan ‘yan ta’addan 280 da suka kunshi maza  29 da mata 73 da kuma kananan yara 148 suka mika wuya.


Kakakin na ma’aikatar tsaron Najeriya ya tabbatar da yadda Sojojin sama da na kasa suka yiwa maboyar ‘yan ta’addan luguden wuta wanda ya kai ga wannan nasara.


A cewarsa ‘yan ta’addan na ISWAP da Boko Haram na boye ne a kananun kauyuka da kuma kan duwatsun da ke yankin na Arewa maso gabas.


Ma’aikatar tsaron Najeriyar ta bayyana cewa a tsawon makwanni 3 da dakarun na ta suka kaddamar da sumame kan maboyar ‘yan ta’addan sun yi nasarar kwato bindigogi kirar AK47 guda 20 kana kirar G3 guda 2 sai kirar FN 5 da kuma QJC 2 sai babbar motar daukar bindiga mai silke sai harsasai dubu 2 da 411 sai kuma wasu harsasai mai alamar NATO kana gurneti 36 da sauran makamai masu hadari.


Sauran abubuwan da dakarun suka kwato daga maboyar ‘yan ta’addan sun kunshi Babura 33 da kekuna 33 sai kayakin kula da lafiya da kuma tarin kayakin sawa dana abinci sai tsabar kudi Naira dubu 291da 60.


A baya-bayannan dai za'a iya cewa rundunar sojin Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen murkushe ayyukan yan ta'adda a arewa maso gabas. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post